bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Jeremiah 18
Jeremiah 18
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 17
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 19 →
1
Ubangiji ya yi magana da Irmiya ya ce,
2
“Ka tashi, ka gangara zuwa gidan maginin tukwane, a can zan yi maka magana.”
3
Sai na gangara zuwa gidan maginin tukwanen, na iske shi yana ginin tukwane a kan na'urar ginin tukwanen.
4
Abin da yake ginawa ya lalace a hannunsa, sai ya sāke gina wani abu dabam da yumɓu ɗin, yadda ya ga dama.
5
Sa'an nan Ubangiji ya ce mini,
6
“Ya jama'ar Isra'ila, ashe, ba zan yi da ku kamar yadda maginin tukwanen nan ya yi ba? Duba, kamar yadda yumɓu yake a hannun maginin tukwane, haka kuke a hannuna, ya ku jama'ar Isra'ila.
7
A duk lokacin da na ce zan tumɓuke, in kakkarya in hallaka wata al'umma, ko wani mulki,
8
idan wannan al'umma da na yi magana a kanta, ta juyo, ta tuba daga mugayen ayyukanta, zan janye masifar da na yi niyyar aukar mata.
9
A duk kuma lokacin da na ce zan gina, in kafa wata al'umma, ko wani mulki,
10
amma idan al'ummar ta aikata mugunta a gabana, ta ƙi saurarawa ga maganar, zan janye alherin da na yi niyyar yi mata.
11
Saboda haka yanzu, sai ka faɗa wa jama'ar Yahuza da mazaunan Urushalima, ka ce, haka Ubangiji ya faɗa, ‘Ga shi, na shirya muku masifa, ina tsara wahalar da za ta same ku. Bari kowannenku ya koma ya bar muguwar hanyarsa, ya gyara al'amuransa da ayyukansa.’
12
Amma za su ce, ‘Wannan ba abin da za mu kula da shi ba ne, mu ra'ayinmu za mu bi, kowannenmu kuwa zai yi bisa ga nufin tattaurar muguwar zuciyarsa.’
13
“Domin haka ni Ubangiji na ce, ‘Ka tambayi sauran al'umma. Wa ya taɓa jin irin wannan? Budurwa Isra'ila, ta yi mugun abu ƙwarai!
14
Dusar ƙanƙara mai danshi ta taɓa rabuwa da tsaunukan Lebanon? Ko ruwan rafuffuka mai sanyi na kan dutse ya taɓa ƙonawa?
15
Amma mutanena sun manta da ni, Sun ƙona wa gumaka turare. Sun yi tuntuɓe a cikin al'amuransu, a hanyoyin dā, Sun bi ɓarayin hanyoyi, ba su bi karauka ba.
16
Sun mai da ƙasarsu abar banƙyama, Abin raini har abada. Duk wanda ya wuce ta wurin zai razana ya kaɗa kansa.
17
Haka zan warwatsa su Kamar yadda iskar gabas take yi, a gaban abokan gābansu, Zan juya musu baya, ba za su ga fuskata ba, A ranar masifarsu.’ ”
18
Sa'an nan suka ce, “Zo mu shirya wa Irmiya maƙarƙashiya, gama firist ba zai bar bin shari'a ba. Haka nan ma masu hikima ba za su bar yin shawara ba, haka nan kuma annabi ba zai bar yin magana ba! Ku zo mu kai ƙararsa, kada mu kula da abin da zai faɗa.”
19
Irmiya kuwa ya yi addu'a ya ce, “Ya Ubangiji, ka kasa kunne gare ni, ka ji ƙarar maƙiyana!
20
Daidai ne a rama alheri da mugunta? Duk da haka sun kafa wa raina tarko. Ka tuna yadda na tsaya a gabanka, Na yi maganar alheri a kansu, Domin ka janye fushinka daga gare su.
21
Saboda haka ka kawo wa 'ya'yansu yunwa, Ka bashe su ga takobi, Bari matansu su rasa 'ya'ya, mazansu su mutu, Ka sa annoba ta kashe mazansu, A kashe samarinsu da takobi a yaƙi.
22
Bari a ji kururuwa daga gidajensu, Saboda maharan da ka aika musu farat ɗaya, Gama sun haƙa rami don in fāɗa, Sun kafa wa ƙafafuna tarkuna.
23
Amma ya Ubangiji, Ka san dukan maƙarƙashiyarsu, su kashe ni, Kada ka gafarta musu muguntarsu, kada kuma ka shafe zunubinsu daga gabanka. Ka sa a jefar da su daga gabanka, Ka yi da su sa'ad da kake fushi!”
← Chapter 17
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 19 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52