bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Jeremiah 5
Jeremiah 5
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 4
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 6 →
1
“Ku bi titunan Urushalima ko'ina! Ku dudduba ku lura! Ku bincika kowane dandali, ku gani, Ko za ku iya samun ko mutum ɗaya Mai aikata adalci, mai son gaskiya, Sai in gafarta mata.
2
Ko da yake suna cewa, ‘Na rantse da ran Ubangiji,’ Duk da haka rantsuwar ƙarya suke yi.”
3
Ya Ubangiji, ashe, ba masu gaskiya kake so ba? Ka buge su, amma ba su yi nishi ba, Ka hore su, amma sun ƙi horuwa, Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse, Sun ƙi tuba.
4
Sai na ce, “Waɗannan mutane ba su da kirki, Ba su da hankali, Ba su san hanyar Ubangiji, Ko shari'ar Allahnsu ba.
5
Zan tafi wurin manyan mutane, in yi musu magana, Gama sun san nufin Ubangiji, da shari'ar Allahnsu.” Amma dukansu sun ƙi yarda Ubangiji ya mallake su, Suka ƙi yi masa biyayya.
6
Domin haka zaki daga kurmi zai kashe su, Kyarkeci kuma daga hamada zai hallaka su. Damisa tana yi wa biranensu kwanto, Duk wanda ya fita daga cikinsu sai a yayyage shi, Domin laifofinsu sun yi yawa, Karkacewarsu babba ce.
7
“Don me zan gafarce ki? 'Ya'yanki sun rabu da ni, Sun yi rantsuwa da gumaka, Na ciyar da su har sun ƙoshi sosai, Suka yi karuwanci, suka ɗunguma zuwa gidajen karuwai,
8
Kamar ƙosassun ingarmu suke, masu jaraba, Kowa yana haniniya, yana neman matar maƙwabcinsa.
9
Ba zan hore su saboda waɗannan abubuwa ba? Ni Ubangiji na ce, ba zan ɗauka wa kaina fansa a kan wannan al'umma ba?
10
Ku haura, ku lalatar da gonar kurangar inabinta, Amma kada ku yi mata ƙarƙaf, Ku sassare rassanta, Gama su ba na Ubangiji ba ne.
11
Gama mutanen Isra'ila da mutanen Yahuza Sun zama marasa aminci a gare ni. Ni Ubangiji na faɗa.”
12
Sun yi ƙarya a kan Ubangiji, Suka ce, “Ba abin da zai yi, Ba wata masifa da za ta same mu. Ba kuwa za mu ga takobi ko yunwa ba.
13
Annabawa holoƙo ne kawai, Maganar ba ta cikinsu. Haka za a yi da su!”
14
Saboda haka Ubangiji Allah Mai Runduna ya ce, “Domin sun hurta wannan magana, Ga shi, zan sa maganata a bakinka ta zama wuta, Waɗannan mutane kuwa su zama itace, Wutar za ta cinye su.
15
“Ya ku mutanen Isra'ila, ga shi, ina kawo muku Wata al'umma daga nesa,” in ji Ubangiji, “Al'umma ce mai ƙarfin hali ta tun zamanin dā. Al'umma wadda ba ku san harshenta ba, Ba za ku fahimci abin da suke faɗa ba.
16
Kwarinsu kamar buɗaɗɗen kabari ne, Dukansu jarumawa ne.
17
Za su cinye amfanin gonakinku da abincinku. Za su ƙare 'ya'yanku mata da maza. Za su cinye garkunanku na tumaki, da na awaki, da na shanu, Za su kuma cinye 'ya'yan inabinku da na ɓaurenku. Za su hallaka biranenku masu kagara da takobi, waɗanda kuke fariya da su.
18
“Amma ko a cikin waɗancan kwanaki ba zan yi muku ƙaƙaf ba,” in ji Ubangiji.
19
“Sa'ad da mutanenki suka ce, ‘Me ya sa Ubangiji Allahnmu ya yi mana waɗannan abubuwa duka?’ sai ki ce musu, ‘Kamar yadda kuka rabu da ni kuka bauta wa gumaka a ƙasarku, haka kuma za ku bauta wa baƙi a ƙasar da ba taku ba.’ ”
20
“Ka sanar wa zuriyar Yakubu da wannan, Ka kuma yi shelarsa a Yahuza, ka ce,
21
‘Ku ji wannan, ya ku wawaye, marasa hankali, Kuna da idanu, amma ba ku gani, Kuna da kunnuwa, amma ba ku ji.’ ”
22
Ubangiji ya ce, “Ba za ku ji tsorona ba? Ba za ku yi rawar jiki a gabana ba? Ni ne na sa yashi ya zama iyakar teku, Tabbatacciyar iyaka, wadda ba ta hayuwa, Ko da yake raƙuman ruwa za su yi hauka, ba za su iya haye ta ba, Ko da suna ruri, ba za su iya wuce ta ba.
23
Amma mutanen nan suna da taurin zuciya, masu halin tayarwa ne, Sun rabu da ni, sun yi tafiyarsu.
24
A zuciya ba su cewa, ‘Bari mu ji tsoron Ubangiji Allahnmu Wanda yake ba mu ruwan sama a kan kari, Na kaka da na bazara, Wanda yake ba mu lokacin girbi.’
25
Laifofinku sun raba ku da waɗannan abubuwa. Zunubanku kuma sun hana ku samun alheri.
26
“Gama an sami mugaye, a cikin jama'ata, Suna kwanto kamar masu kafa ashibta. Sun ɗana tarko su kama mutane.
27
Kamar kwando cike da tsuntsaye, Haka nan gidajensu suke cike da cin amana, Don haka suka zama manya, suka sami dukiya.
28
Sun yi ƙiba, sun yi bul-bul, Ba su da haram a kan aikata mugunta, Ba su yi wa marayu shari'ar adalci, don kada su taimake su. A wajen shari'a ba su bin hakkin matalauta.
29
“Ba zan hukunta su saboda waɗannan abubuwa ba? Ba zan ɗaukar wa kaina fansa a kan al'umma irin wannan ba?
30
“Abin banmamaki da bantsoro Ya faru a ƙasar.
31
Annabawa sun yi annabcin ƙarya, Firistoci kuma sun yi mulki da ikon kansu, Mutanena kuwa suna so haka! Amma sa'ad da ƙarshe ya zo, me za ku yi?”
← Chapter 4
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 6 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52