bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Jeremiah 46
Jeremiah 46
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 45
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 47 →
1
Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan sauran al'umma.
2
Ya yi magana game da sojojin Fir'auna, Sarkin Masar, waɗanda suke a bakin Kogin Yufiretis a Karkemish, waɗanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya ci su da yaƙi a shekara ta huɗu ta sarautar Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza.
3
Masarawa suka yi ihu, suka ce, “Ku shirya kutufani da garkuwa, Ku matso zuwa wurin yaƙi!
4
Ku ɗaura wa dawakanku sirdi, ku hau! Ku tsaya a wurarenku da kwalkwali a ka! Ku wasa māsunku! Ku sa kayan yaƙi!”
5
Ubangiji ya yi tambaya ya ce, “Me nake gani? Sun tsorata, suna ja da baya, An ci sojojinsu, suna gudu, Ba su waiwayen baya, akwai tsoro a kowane sashi.”
6
Masu saurin gudu ba za su tsere ba, Haka nan kuma jarumi, A arewa a gefen Kogin Yufiretis, Sun yi tuntuɓe, sun fādi.
7
Wane ne wannan mai tashi kamar Kogin Nilu, Kamar kogunan da ruwansu yake ambaliya?
8
Masar tana tashi kamar Nilu, Kamar kogunan da ruwansu yake ambaliya. Masar ta ce, “Zan tashi, in rufe duniya, Zan hallaka birane da mazauna cikinsu.”
9
Ku haura, ku dawakai, Ku yi sukuwar hauka, ku karusai! Bari sojoji su fito, Mutanen Habasha da Fut masu riƙon garkuwoyi, Da mutanen Lud, waɗanda suka iya riƙon baka.
10
Wannan rana ta Ubangiji, Allah Mai Runduna ce, Ranar ɗaukar fansa ce don ya rama wa maƙiyansa. Takobi zai ci, ya ƙoshi, Ya kuma sha jininsu, ya ƙoshi, Gama Ubangiji Allah Mai Runduna zai hallaka maƙiyansa, A arewa, a bakin Kogin Yufiretis.
11
Ku mutanen Masar, ku haura zuwa Gileyad Don ku samo ganye! A banza kuke morar magunguna, Ba za ku warke ba.
12
Kunyarku ta kai cikin sauran al'umma, Kukanku kuma ya cika duniya. Soja na faɗuwa bisa kan soja. Dukansu biyu sun faɗi tare.
13
Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan zuwan Nebukadnezzar, Sarkin Babila, don ya yi yaƙi da ƙasar Masar.
14
“Ku yi shelarsa cikin garuruwan Masar, Cikin Migdol, da Memfis, da Tafanes, Ku ce, ‘Ku tsaya, ku yi shiri, Gama takobi yana cin waɗanda suke kewaye da ku!’
15
Me ya sa gunkinka, Afis, ya fāɗi, Wato bijimi, gunkinka bai tsaya ba? Domin Ubangiji ya tunkuɗe shi ƙasa!
16
Sun yi ta fāɗuwa, Suna faɗuwa a kan juna, Sai suka ce, ‘Mu tashi mu koma wurin mutanenmu, Zuwa ƙasar haihuwarmu, mu gudu daga takobin azzalumi!’
17
“Ku ba Fir'auna Sarkin Masar sabon suna, ‘Mai yawan surutu, wanda bai rifci zarafi ba!’
18
Ni wanda sunana Ubangiji Mai Runduna Sarki ne, Na rantse da raina, wani zai ɓullo, Kamar Tabor a cikin tsaunuka, Ko kuwa kamar Karmel a bakin teku.
19
Ya ku mazaunan Masar, Ku shirya kayanku don zuwa bauta, Gama Memfis za ta lalace, ta zama kufai, Ba mai zama a ciki.
20
“Masar kyakkyawar karsana ce, Amma bobuwa daga arewa ta aukar mata!
21
Sojojin ijararta kamar 'yan maruƙa ne, masu yawan kitse, Sun ba da baya, sun gudu, ba su tsaya ba, Domin ranar masifarsu ta zo, Lokacin halakarsu ya yi.
22
Masar tana gudu, tana huci kamar maciji, Gama abokan gābanta suna zuwa da ƙarfi, Za su faɗo mata da gatura kamar masu saran itatuwa.
23
Ni Ubangiji na ce, za su sari kurminta, Ko da yake ba su ƙirguwa, Gama suna da yawa kamar fara, Ba su lasaftuwa.
24
Za a kunyatar da mutanen Masar, An bashe su a hannun mutanen arewa.”
25
Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “Ga shi, zan hukunta Amon na No, da Fir'auna, da Masar, tare da allolinta, da sarakunanta, wato Fir'auna, tare da waɗanda suke dogara gare shi.
26
Zan bashe su a hannun waɗanda suke neman ransu, wato a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, da shugabanninsa. Daga baya kuma mutane za su zauna a Masar kamar dā. Ni Ubangiji na faɗa.
27
“Ya bawana Yakubu, kada ka ji tsoro, Kada ka firgita, ya Isra'ila. Gama zan cece ka daga ƙasa mai nisa, Zan ceci zuriyarka daga ƙasar bautarsu. Yakubu zai komo, ya yi zamansa da rai kwance, Ba wanda zai razanar da shi.
28
Ni Ubangiji na ce, Kada ka ji tsoro, ya bawana Yakubu, Gama ina tare da kai. Zan hallaka dukan sauran al'umma sarai inda na kora ka. Amma ba zan hallaka ka sarai ba. Zan hukunta ka yadda ya kamata, Ba zan bar ka ba hukunci ba.”
← Chapter 45
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 47 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52