bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Jeremiah 14
Jeremiah 14
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 13
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 15 →
1
Maganar da Ubangiji ya yi wa Irmiya a kan fari ke nan,
2
“Yahuza tana makoki, Ƙofofin biranenta suna lalacewa, Mutanenta suna kwance a ƙasa, suna makoki, Urushalima tana kuka da babbar murya.
3
Manyan mutanenta sun aiki barorinsu su ɗebo ruwa. Da suka je maɓuɓɓuga, sai suka tarar ba ruwa. Sai suka koma da tulunansu haka nan, An kunyatar da su, an ƙasƙantar da su, Suka lulluɓe kansu don kunya.
4
Saboda ƙasar ta bushe, Tun da ba a yi ruwa a kanta ba, Manoma sun sha kunya, Suka lulluɓe kansu don kunya.
5
Barewa ma a saura takan gudu, Ta bar ɗanta sabon haihuwa, Domin ba ciyawa.
6
Jakunan jeji suna tsaye a kan tuddan da ba ciyawa, Suna haki kamar diloli, Idanunsu ba su gani Domin ba abinci.”
7
Irmiya ya ce, “Ko da yake zunubanmu su ne shaidunmu, Ya Ubangiji, ka yi taimako saboda sunanka! Gama kāsawarmu ta yi yawa, Domin mun yi maka zunubi.
8
Ya kai, wanda kake begen Isra'ila, Mai Cetonta a lokacin wahala, Ƙaƙa ka zama kamar baƙo a ƙasar? Kamar matafiyi wanda ya kafa alfarwarsa a gefen hanya don ya kwana, ya wuce?
9
Ƙaƙa ka zama kamar wanda bai san abin da zai yi ba, Kamar jarumin da ya kasa yin ceto? Duk da haka, ya Ubangiji, kana nan a tsakiyarmu. Da sunanka ake kiranmu, Kada ka bar mu!”
10
Haka Ubangiji ya ce a kan waɗannan mutane, “Sun cika son yawaceyawace, ba su iya zama wuri ɗaya, don haka ni Ubangiji, ban yarda da su ba, zan tuna da laifofinsu in hukunta zunubansu.”
11
Sai Ubangiji ya ce mini, “Kada ka yi addu'a domin lafiyar jama'an nan.
12
Ko da sun yi azumi, ba zan ji kukansu ba, ko da sun miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta sha, ba zan karɓe su ba. Amma zan hallaka su da takobi, da yunwa, da annoba.”
13
Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah, ga shi, annabawa sun faɗa musu, sun ce, ‘Ba za ku ga takobi ko yunwa ba, amma zan ba ku dawwamammiyar salama a wannan wuri.’ ”
14
Ubangiji kuwa ya ce mini, “Annabawa, annabcin ƙarya suka yi da sunana. Ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba, ban kuma yi magana da su ba. Annabcin da suke yi muku na wahayin ƙarya ne, dubar da suke yi marar amfani ce, tunaninsu ne kawai.
15
Domin haka ga abin da ni Ubangiji na ce a kan annabawan da suke yin annabci da sunana, ko da yake ban aike su ba, waɗanda suke cewa, ‘Takobi da yunwa ba za su shigo ƙasan nan ba.’ Za a hallaka su da takobi da yunwa.
16
Mutanen da suka yi wa annabci, za a jefar da su waje a kan titunan Urushalima, a karkashe su da yunwa da takobi, ba wanda zai binne su, da su, da matansu, da 'ya'yansu mata da maza. Zan sa muguntarsu ta koma kansu.
17
“Irmiya, ka faɗa wa mutanen baƙin ciki da ya same ka, Ka ce, ‘Bari idanuna su yi ta zub da hawaye dare da rana, Kada su daina, saboda an buge budurwa, 'yar jama'ata, An yi mata babban rauni da dūka mai tsanani.
18
Idan na tafi cikin saura, Sai in ga waɗanda aka kashe da takobi! Idan kuma na shiga birni, Sai in ga waɗanda suke ta fama da yunwa! Gama annabi da firist, sai harkarsu suke ta yi a ƙasar, Amma ba su san abin da suke yi ba.’ ”
19
“Ka ƙi Yahuza ke nan ɗungum? Ranka kuma yana jin ƙyamar Sihiyona ne? Me ya sa ka buge mu, har da ba za mu iya warkewa ba? Mun zuba ido ga samun salama, amma ba wani abin alheri da ya zo. Mun kuma sa zuciya ga warkewa, amma sai ga razana.
20
Mun san muguntar da muka yi, ya Ubangiji, Da wadda kakanninmu suka yi, Gama mun yi maka zunubi.
21
Saboda darajar sunanka, kada ka wulakanta mu, Kada kuma ka ƙasƙantar da darajar kursiyinka, Ka tuna da alkawarin da ka yi mana, Kada ka ta da shi.
22
A cikin gumakan al'ummai akwai mai iya sa a yi ruwa? Sammai kuma su yi yayyafi? Ashe, ba kai ne ba, ya Ubangiji Allahnmu? Domin haka a gare ka muke sa zuciya, Gama kai ne mai yin waɗannan abubuwa duka.”
← Chapter 13
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 15 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52