bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Genesis 13
Genesis 13
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 12
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 14 →
1
Domin haka Abram ya bar Masar zuwa Negeb, shi da matarsa, da abin da yake da shi duka tare da Lutu.
2
Yanzu Abram ya arzuta da dabbobi, da azurfa, da zinariya.
3
Ya yi ta tafiya daga Negeb har zuwa Betel, har wurin da ya kafa alfarwarsa da fari, tsakanin Betel da Ai,
4
a inda dā ya gina bagade. A can Abram ya kira bisa sunan Ubangiji.
5
Lutu wanda ya tafi tare da Abram, shi kuma yana da garkunan tumaki, da na shanu, da alfarwai,
6
domin haka ƙasar ba ta isa dukansu biyu su zauna tare ba, saboda mallakarsu ta cika yawa, har da ba za su iya zama tare ba.
7
Akwai rashin jituwa kuma a tsakanin makiyayan dabbobin Abram da makiyayan dabbobin Lutu. Mazaunan ƙasar, a lokacin nan Kan'aniyawa da Ferizziyawa ne.
8
Abram ya ce wa Lutu, “Kada rashin jituwa ya shiga tsakanina da kai ko tsakanin makiyayanka da nawa, gama mu 'yan'uwa ne.
9
Ba ƙasar duka tana gabanka ba? Sai ka ware daga gare ni. In ka ɗauki hagu in ɗauki dama, in kuwa ka ɗauki dama ni sai in ɗauki hagu.”
10
Lutu ya ɗaga idanunsa sama ya dubi kwarin Urdun, ga shi kuwa da dausayi mai kyau ƙwarai, sai ka ce gonar Ubangiji, kamar ƙasar Masar wajen Zowar, tun kafin Allah ya hallaka Saduma da Gwamrata.
11
Domin haka, Lutu ya zaɓar wa kansa kwarin Urdun duka, Lutu kuma ya kama hanya ya nufi gabas. Haka fa suka rabu da juna.
12
Abram ya zauna a ƙasar Kan'ana, Lutu kuwa ya zauna a biranen kwari, ya zakuɗar da alfarwarsa har zuwa Saduma.
13
Mutanen Saduma kuwa mugaye ne masu aikata zunubi ƙwarai gāba da Ubangiji.
14
Sai Ubangiji ya ce wa Abram, bayan da Lutu ya rabu da shi, “Ɗaga idanunka sama, daga inda kake, ka dubi kusurwoyin nan huɗu,
15
gama dukan ƙasan nan da kake gani kai zan ba, da zuriyarka har abada.
16
Zan mai da zuriyarka kamar turɓayar ƙasa, har in mutum ya iya ƙidaya turɓayar ƙasa, to, a iya ƙidaya zuriyarka.
17
Tashi, ka yi tafiya cikin ratar ƙasar da fāɗinta, gama zan ba ka ita.”
18
Sai Abram ya cire alfarwarsa, ya zo ya zauna kusa da itatuwan oak na Mamre, waɗanda suke Hebron. A can ya gina wa Ubangiji bagade.
← Chapter 12
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 14 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50