bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Genesis 23
Genesis 23
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 22
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 24 →
1
Saratu ta yi shekara ɗari da ashirin da bakwai a duniya,
2
sa an nan ta rasu a Kiriyat-arba, wato Hebron, a ƙasar Kan'ana. Ibrahim kuwa ya tafi ya yi makoki, yana baƙin ciki domin Saratu.
3
Ibrahim ya bar gawar matarsa, ya je ya ce wa Hittiyawa,
4
“Ni baƙo ne, ina tsakaninku, ina zaman baƙunci. Ku sayar mini da wurin yin makabarta, domin in binne matata, in daina ganinta!”
5
Hittiyawa suka amsa wa Ibrahim suka ce,
6
“Ka ji mu, ya shugaba, gama kai yardajjen Allah ne a tsakaninmu. Ka binne matarka a kabari mafi kyau na kaburburanmu, ba waninmu da zai hana maka kabarinsa, ko ya hana ka ka binne matarka.”
7
Ibrahim ya tashi ya sunkuya wa Hittiyawa, mutanen ƙasar.
8
Sai ya ce musu, “Idan kun yarda in binne matata in daina ganinta, to, ku ji ni, ku roƙar mini Efron Bahitte ɗan Zohar,
9
ya ba ni kogon Makfela nasa na can ƙarshen saurarsa. Bari ya sallama mini wurin a gabanku a cikakken kuɗinsa, ya zama mallakata domin makabarta.”
10
A sa'an nan Efron yana tare da Hittiyawa. Sai Efron Bahitte ya amsa wa Ibrahim a kunnuwan Hittiyawa, da gaban dukan waɗanda suke shiga ta ƙofar birninsa, ya ce,
11
“Ba haka ba ne, ya shugaba, ka ji ni. Na ba ka saurar, da kogon da yake cikinta. A gaban jama'ata na ba ka ita, ka binne matarka.”
12
Ibrahim kuwa ya sunkuya a gaban jama'ar ƙasar.
13
Ya ce wa Efron, a kunnuwan jama'ar ƙasar, “In dai ka yarda, ka ji ni. Zan ba da kuɗin saurar. Ka karɓa daga gare ni don in binne matata a can.”
14
Efron ya amsa wa Ibrahim,
15
“Ya shugabana, ka ji ni, don ɗan yankin ƙasa na shekel ɗari huɗu, a bakin me yake, a tsakaninmu? Binne matarka.”
16
Ibrahim ya yarda da Efron. Ibrahim kuwa ya auna wa Efron yawan shekel da ya ambata a kunnuwan Hittiyawa, shekel ɗari huɗu bisa ga nauyin da 'yan kasuwa suke amfani da shi a wancan lokaci.
17
Don haka saurar Efron da yake cikin Makfela wadda take gabashin Mamre, da saurar, da kogon da yake ciki, da dukan itatuwan da suke cikin saurar, iyakar girmanta duka
18
an tabbatar wa Ibrahim, cewa mallakarsa ce a gaban Hittiyawa, a gaban dukan waɗanda suke shiga ta ƙofar birninsu.
19
Bayan wannan, Ibrahim ya binne Saratu matarsa a kogon da yake a saurar Makfela a gabashin Mamre, wato Hebron, cikin ƙasar Kan'ana.
20
Da saurar, da kogon da yake cikinta, aka tabbatar wa Ibrahim mallakarsa ce don makabarta da iznin Hittiyawa.
← Chapter 22
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 24 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50