bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Genesis 4
Genesis 4
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 3
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 5 →
1
Adamu kuwa ya san matarsa Hawwa'u, ta kuwa yi ciki, ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Na sami ɗa namiji da iznin Ubangiji.”
2
Ta kuma haifi ɗan'uwansa Habila. Habila makiyayin tumaki ne, Kayinu kuwa manomi ne.
3
Wata rana, sai Kayinu ya kawo sadaka ga Ubangiji daga amfanin gona.
4
Habila kuwa ya kawo nasa ƙosassu daga cikin 'ya'yan fari na garkensa. Ubangiji kuwa ya kula da Habila da sadakarsa,
5
amma Kayinu da sadakarsa, bai kula da su ba. Saboda haka Kayinu ya husata ƙwarai, har tsikar jikinsa ta tashi.
6
Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Me ya sa ka husata, me kuma ya sa har tsikar jikinka ta tashi?
7
In da ka yi daidai, ai, da ka yi murmushi. Amma tun da ka yi mugunta, to, zunubi zai yi fakonka don ya rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so ya mallake ka, amma tilas ne ka rinjaye shi.”
8
Kayinu ya ce wa ɗan'uwansa Habila, “Mu tafi cikin saura.” A lokacin da suke cikin saura, sai Kayinu ya tasar wa ɗan'uwansa Habila, har ya kashe shi.
9
Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina Habila ɗan'uwanka?” Ya ce, “Ban sani ba, ni makiyayin ɗan'uwana ne?”
10
Sai Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Muryar jinin ɗan'uwanka tana yi mini kuka daga ƙasa.
11
Yanzu fa, kai la'ananne ne daga cikin ƙasar da ta buɗe baki, ta karɓi jinin ɗan'uwanka daga hannunka.
12
In ka yi noma, ƙasar ba za ta ƙara ba ka cikakken amfaninta ba, za ka zama mai yawo barkatai, mai kai da kawowa a duniya.”
13
Kayinu ya ce wa Ubangiji, “Hukuncina ya fi ƙarfina.
14
Ga shi, yanzu ka kore ni a guje daga fuskar ƙasar, zan zama a ɓoye daga fuskarka, zan kuma zama mai yawo barkatai, mai kai da kawowa a duniya, duk wanda ya same ni kuwa zai kashe ni.”
15
Sai Ubangiji ya ce masa, “Ba haka ba ne! Wanda duk ya kashe Kayinu, za a rama masa har sau bakwai.” Ubangiji kuma ya sa wa Kayinu tabo, domin duk wanda ya iske shi kada ya kashe shi.
16
Kayinu ya yi tafiyarsa ya rabu da Ubangiji, ya zauna a ƙasar Nod, gabashin Aidan.
17
Kayinu ya san matarsa, ta kuwa yi ciki ta haifi Anuhu, ya kuwa gina birni ya sa wa birnin sunan ɗansa, Anuhu.
18
An haifa wa Anuhu ɗa, wato Airad. Airad ya haifi Mehuyayel, Mehuyayel kuwa ya haifi Metushayel, Metushayel kuma ya haifi Lamek.
19
Lamek ya auri mata biyu, sunan ɗayar Ada, ta biyun kuwa Zulai.
20
Ada ta haifi Yabal, shi ne ya zama uban mazaunan alfarwa, makiyayan dabbobi.
21
Sunan ɗan'uwansa Yubal, wanda ya zama uban makaɗan garaya da mabusan sarewa.
22
Zulai kuwa ta haifi Tubal-kayinu, shi ne asalin maƙeran dukan kayayyakin tagulla da na baƙin ƙarfe. Sunan 'yar'uwar Tubalkayinu Na'ama ne.
23
Lamek kuwa ya ce wa matansa, “Ada da Zulai, ku ji muryata, ku matan Lamek ku ji abin da nake cewa na kashe mutum domin ya yi mini rauni, saurayi kuma don ya buge ni.
24
Idan an rama wa Kayinu sau bakwai, hakika na Lamek, sai sau saba'in da bakwai.”
25
Sai kuma Adamu ya san matarsa, ta kuwa haifi ɗa, ta raɗa masa suna Shitu, gama ta ce, “Allah ya arzuta ni da ɗa maimakon Habila wanda Kayinu ya kashe.”
26
Ga Shitu kuma aka haifi ɗa, ya kuwa raɗa masa suna Enosh. A wannan lokaci ne mutane suka fara kira bisa sunan Ubangiji.
← Chapter 3
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 5 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
Recommended Reading
Commentary
Genesis Commentaries
→
Devotional
Genesis Devotional Guide
→
Get This Bible
Hausa Bible (Littafi Mai Tsarki) Study Bible
→