bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Genesis 44
Genesis 44
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 43
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 45 →
1
Yusufu ya umarci mai hidimar gidansa, ya ce, “Cika tayakan mutanen nan da abinci iyakar yadda za su iya ɗauka, ka kuma sa kuɗin kowanne a bakin taikinsa,
2
ka sa finjalina na azurfa a bakin taikin autan, tare da kuɗinsa na hatsin.” Sai ya yi kamar yadda Yusufu ya faɗa masa.
3
Gari na wayewa aka sallami mutanen da jakunansu.
4
Tun ba su riga suka yi nisa da garin ba, Yusufu ya ce wa mai hidimar gidansa, “Tashi, ka bi mutanen, in ka iske su ka ce musu,
5
‘Don me kuka rama alheri da mugunta? Don me kuka sace mini finjalina na azurfa? Da shi ne mai gidana yake sha, da shi ne kuma yake yin istihara. Kun yi kuskure da kuka yi haka.’ ”
6
Lokacin da ya iske su sai ya yi musu waɗannan maganganu.
7
Suka ce masa, “Don me shugabana zai faɗi irin waɗannan maganganu? Allah ya sawwaƙe da bayinka za su aikata irin wannan!
8
Ga shi, kuɗin da muka samu a bakin tayakanmu, mun komo maka da su tun daga ƙasar Kan'ana, ta yaya fa, za mu saci azurfa ko zinariya daga gidan maigidanka?
9
Daga cikinmu barorinka, duk wanda aka sami abin a wurinsa, bari ya mutu, mu kuwa mu zama bayinka, ranka ya daɗe.”
10
Ya ce, “Bari ya zama kamar yadda kuka faɗa, shi wanda aka sami abin a wurinsa zai zama bawana, sauranku kuwa za ku tafi lafiya.”
11
Nan da nan kowa ya saukar da taikinsa ƙasa, kowa kuwa ya buɗe taikinsa.
12
Ya bincika, ya fara daga babba zuwa ƙarami, sai aka iske finjalin a cikin taikin Biliyaminu.
13
Suka kyakkece rigunansu, kowannensu kuwa ya yi wa jakinsa labtu suka koma birnin.
14
Sa'ad da Yahuza da 'yan'uwansa suka zo gidan Yusufu, suka iske yana nan har yanzu, sai suka fāɗi ƙasa a gabansa.
15
Yusufu ya ce musu, “Wane abu ke nan kuka aikata? Ba ku sani ba, mutum kamata yakan yi istihara?”
16
Sai Yahuza ya amsa, “Me za mu ce wa shugabana? Wace magana za mu yi? Ko kuwa, ta yaya za mu baratar da kanmu? Allah ne ya tona laifin bayinka, ga mu, mu bayin shugabana ne, da mu da shi wanda aka sami finjalin a wurinsa.”
17
Amma Yusufu ya ce, “Allah ya sawwaƙe mini da in yi haka! Sai shi wanda aka sami finjalin a hannunsa, shi zai zama bawana, amma ku, ku yi tafiyarku lafiya zuwa wurin mahaifinku.”
18
Yahuza ya je wurin Yusufu ya ce, “Ya shugabana, ina roƙonka, ka bar bawanka ya yi magana a kunnuwanka, kada kuma ka bar fushinka ya yi ƙuna bisa bawanka, gama daidai da Fir'auna kake.
19
Ranka ya daɗe, ka tambaye mu, ka ce, ‘Kuna da mahaifi ko ɗan'uwa?’
20
Sai muka amsa, ranka ya daɗe, muka ce, ‘Muna da mahaifi, tsoho, da ɗan tsufansa, auta, wanda ɗan'uwansa ya rasu, shi kaɗai ya ragu daga cikin mahaifiyarsa, mahaifinsa kuwa yana ƙaunarsa.’
21
Sai ka ce wa barorinka, ‘Ku kawo shi wurina, don in gan shi.’
22
Ranka ya daɗe, muka kuwa ce, ‘Saurayin ba zai iya rabuwa da mahaifinsa ba, gama in ya rabu da mahaifinsa, mahaifinsa zai mutu.’
23
Sai ka amsa wa barorinka, ka ce, ‘In ba autanku ya zo tare da ku ba, ba za ku ƙara ganin fuskata ba.’
24
“Sa'ad da muka koma a wurin baranka, mahaifinmu, muka mayar masa da dukan abin da ka ce.
25
Don haka sa'ad da mahaifinmu ya ce, ‘Koma, ku sayo mana ɗan abinci,’
26
sai muka ce, ‘Ba za mu iya gangarawa ba, amma idan autanmu zai tafi tare da mu, za mu gangara, gama ba dama mu ga fuskar mutumin sai ko autanmu yana tare da mu.’
27
Sa'an nan baranka, mahaifinmu, ya ce mana, ‘Kun sani 'ya'ya biyu matata ta haifa mini,
28
ɗayan ya bar ni, na kuwa ɗauka, hakika an yayyage shi kaca kaca, gama ban ƙara ganinsa ba.
29
In kuka ɗauke wannan kuma daga gare ni, mai yiwuwa ne a kashe shi, to, za ku sa baƙin ciki ya ishe ni, da tsufana, har ya kashe ni.’
30
“Domin haka kuwa, yanzu, idan na koma wurin baranka, mahaifina, ba tare da saurayin ba, in har bai ga yaron tare da ni ba, zai mutu, gama ransa ya shaƙu da saurayin, barorinka kuwa za su sa baranka, mahaifinmu, ya mutu cikin baƙin ciki, da tsufansa.
32
Gama ni baranka na ɗauki lamunin saurayin wurin mahaifinsa da cewa, ‘In ban komo maka da shi ba, sai alhakinsa ya zauna a kaina a gaban mahaifina duka raina.’
33
Domin haka fa, ina roƙonka, bari ni baranka in zama bawa gare ka, shugabana, a maimakon saurayin a bar saurayin ya koma tare da 'yan'uwansa.
34
Gama yaya zan iya komawa wurin mahaifina, in saurayin ba ya tare da ni? Ina jin tsoron ganin ɓarnar da za ta auko wa mahaifina.”
← Chapter 43
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 45 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50