bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Genesis 5
Genesis 5
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 4
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 6 →
1
Wannan shi ne littafin asalin Adamu. A sa'ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin siffar Allah.
2
Namiji da ta mace ya halicce su, ya sa musu albarka, ya sa musu suna, Mutum, sa'ad da aka halicce su.
3
Da Adamu ya yi shekara ɗari da talatin, ya haifi ɗa cikin kamanninsa da cikin siffarsa, ya kuwa sa masa suna Shitu.
4
Bayan da Adamu ya haifi ɗansa Shitu, ya yi shekara ɗari takwas, sa'an nan ya haifi 'ya'ya mata da maza.
5
Haka nan kuwa dukan kwanakin Adamu shekara ce ɗari tara da talatin, ya rasu.
6
Da Shitu ya yi shekara ɗari da biyar, ya haifi Enosh.
7
Bayan da Shitu ya haifi Enosh ya rayu shekara ɗari takwas da bakwai, ya haifi 'ya'ya mata da maza.
8
Haka nan kuwa dukan kwanakin Shitu shekara ce ɗari tara da goma sha biyu, ya rasu.
9
Da Enosh ya yi shekara tasa'in, ya haifi Kenan.
10
Bayan Enosh ya haifi Kenan ya rayu shekara ɗari takwas da goma sha biyar, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
11
Haka nan kuwa dukan kwanakin Enosh shekara ce ɗari tara da biyar, ya rasu.
12
Sa'ad da Kenan ya yi shekara saba'in, ya haifi Mahalalel.
13
Bayan da Kenan ya haifi Mahalalel ya yi shekara ɗari takwas da arba'in, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
14
Haka nan kuwa dukan kwanakin Kenan shekara ce ɗari tara da goma, ya rasu.
15
Sa'ad da Mahalalel ya yi shekara sittin da biyar ya haifi Yared.
16
Bayan da Mahalalel ya haifi Yared, ya yi shekara ɗari takwas da talatin, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.
17
Haka nan kuwa dukan kwanakin Mahalalel shekara ce ɗari takwas da tasa'in da biyar, ya rasu.
18
Sa'ad da Yared ya yi shekara ɗari da sittin da biyu, ya haifi Anuhu.
19
Bayan da Yared ya haifi Anuhu ya yi shekara ɗari takwas ya haifi 'ya'ya mata da maza.
20
Haka nan kuwa dukan kwanakin Yared shekara ce ɗari tara da sittin da biyu, ya rasu.
21
Sa'ad da Anuhu ya yi shekara sittin da biyar, ya haifi Metusela.
22
Bayan da Anuhu ya haifi Metusela, ya yi tafiya tare da Allah shekara ɗari uku ya haifi 'ya'ya mata da maza.
23
Haka nan kuwa dukan kwanakin Anuhu shekara ce ɗari uku da sittin da biyar.
24
Anuhu ya yi tafiya tare da Allah, Allah kuwa ya ɗauke shi, ba a ƙara ganinsa ba.
25
Sa'ad da Metusela ya yi shekara ɗari da tamanin da bakwai, ya haifi Lamek.
26
Bayan da Metusela ya haifi Lamek ya yi shekara ɗari bakwai da tamanin da biyu, ya haifi 'ya'ya mata da maza.
27
Haka nan kuwa dukan kwanakin Metusela shekara ce ɗari tara da sittin da tara, ya rasu.
28
Sa'ad da Lamek ya yi shekara ɗari da tamanin da biyu, ya haifi ɗa,
29
ya sa masa suna Nuhu, yana cewa, “Daga gare shi za mu sami sauƙin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la'anta.”
30
Bayan da Lamek ya haifi Nuhu ya yi shekara ɗari biyar da tasa'in da biyar, ya haifi 'ya'ya mata da maza.
31
Haka nan kuwa dukan kwanakin Lamek shekara ce ɗari bakwai da saba'in da bakwai, ya rasu.
32
Sa'ad da Nuhu ya yi shekara ɗari biyar, ya haifi Shem, da Ham, da Yafet.
← Chapter 4
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 6 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50