bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Genesis 26
Genesis 26
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 25
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 27 →
1
Aka sāke yin yunwa a ƙasar, banda wadda aka yi a zamanin Ibrahim. Sai Ishaku ya tafi Gerar wurin Abimelek, Sarkin Filistiyawa.
2
Ubangiji kuwa ya bayyana gare shi, ya ce, “Kada ka gangara zuwa Masar, ka zauna a ƙasar da zan faɗa maka.
3
Ka yi baƙunci cikin wannan ƙasa, ni kuwa zan kasance tare da kai, zan sa maka albarka, gama a gare ka da zuriyarka ne na ba da waɗannan ƙasashe, zan kuwa cika rantsuwar da na yi wa Ibrahim mahaifinka.
4
Zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sararin sama, zan kuwa ba zuriyarka dukan waɗannan ƙasashe, ta wurin zuriyarka kuma al'umman duniya duka za su sami albarka,
5
saboda Ibrahim ya yi biyayya da muryata, ya kuma kiyaye umarnina, da dokokina, da ka'idodina, da shari'una.”
6
Ishaku ya yi zamansa a Gerar.
7
Sa'ad da mutanen wurin suka tambaye shi matarsa, ya ce, “Ita 'yar'uwata ce,” gama yana jin tsoro ya ce, “Ita matata ce,” don kada mutanen wurin su kashe shi saboda Rifkatu, da yake ita kyakkyawa ce.
8
Sa'ad da ya dakata 'yan kwanaki a can, sai Abimelek, Sarkin Filistiyawa ya duba ta taga, ya ga Ishaku ya rungumi Rifkatu.
9
Sai Abimelek ya kira Ishaku, ya ce, “Ashe lalle ita matarka ce, ƙaƙa fa ka ce, ‘Ita 'yar'uwata ce’?” Ishaku ya amsa masa ya ce, “Don na yi tsammani zan rasa raina saboda ita.”
10
Abimelek ya ce, “Me ke nan ka yi mana? Ai, da wani daga jama'a ya kwana da matarka a sawwaƙe, da ka jawo laifi a bisanmu.”
11
Abimelek ya umarci dukan mutane ya ce, “Duk wanda ya taɓa mutumin nan ko matarsa, za a kashe shi.”
12
Ishaku ya yi shuka a waccan ƙasar, a shekaran nan kuwa ya girbe cikakken amfani. Ubangiji ya sa masa albarka,
13
har mutumin ya arzuta, ya yi ta haɓaka har ya zama attajiri.
14
Da yake ya yi ta arzuta da garken tumaki, da na shanu, da iyali masu yawa, Filistiyawa suka ji ƙyashinsa.
15
Saboda haka, Filistiyawa don kishi sai suka ciccike rijiyoyin da ƙasa, waɗanda barorin mahaifinsa, Ibrahim, suka haƙa tun Ibrahim yana da rai.
16
Abimelek kuwa ya ce wa Ishaku, “Fita daga cikinmu, gama ka fi ƙarfinmu.”
17
Don haka Ishaku ya bar wurin, ya yi zango cikin kwarin Gerar, ya yi zamansa a can.
18
Sai Ishaku ya sāke haƙa rijiyoyi waɗanda dā aka haƙa a zamanin Ibrahim mahaifinsa, gama Filistiyawa sun tattoshe su bayan rasuwar Ibrahim. Ishaku kuma ya sa wa rijiyoyin sunayen da mahaifinsa ya sa musu.
19
Amma sa'ad da barorin Ishaku suka haƙa rijiya a kwarin, sai suka tarar da idon ruwa.
20
Makiyayan Gerar kuwa suka yi faɗa da makiyayan Ishaku, suna cewa,“Ruwan namu ne.” Saboda haka Ishaku ya sa wa rijiyar suna Esek, domin sun yi jayayya a kanta.
21
Suka haƙa wata rijiya, suka yi jayayya a kan wannan kuma, ya sa mata suna Sitna.
22
Sai ya zakuɗa daga nan ya haƙa wata rijiya kuma, amma ba su yi jayayya a kan wannan ba, don haka ya sa mata suna Rehobot, yana cewa, “Gama yanzu Ubangiji ya yalwata mana, za mu hayayyafa a ƙasa.”
23
Daga nan ya haura zuwa Biyer-sheba.
24
Da daren nan Ubangiji ya bayyana gare shi ya ce, “Ni ne Allah na mahaifinka, kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai, zan sa maka albarka in riɓaɓɓanya zuriyarka saboda bawana Ibrahim.”
25
Ishaku ya gina bagade a wurin ya kira bisa sunan Ubangiji, a can kuwa ya kafa alfarwarsa. A can ne kuma barorin Ishaku suka haƙa rijiya.
26
Abimelek ya zo daga Gerar tare da Ahuzat mashawarcinsa da Fikol shugaban sojojinsa, don ya ga Ishaku.
27
Sai Ishaku ya ce musu, “Me yake tafe da ku zuwa gare ni, ga shi kun ƙi ni, kun kuma kore ni nesa da ku?”
28
Suka ce, “Lalle, mun gani a fili Ubangiji yana tare da kai, saboda haka muke cewa bari rantsuwa ta kasance tsakaninmu da kai, bari kuma mu ƙulla alkawari da kai,
29
cewa ba za ka cuce mu ba, daidai kamar yadda ba mu taɓe ka ba, ba mu yi maka kome ba sai alheri, muka kuwa sallame ka cikin salama. Yanzu, kai albarkatacce ne na Ubangiji.”
30
Sai ya shirya musu liyafa, suka ci suka sha.
31
Suka tashi tun da sassafe suka rantse wa juna, Ishaku ya sallame su, suka tafi cikin salama.
32
Ya zama kuwa a wannan rana, barorin Ishaku suka zo suka faɗa masa zancen rijiyar da suka haƙa, suka ce masa, “Mun sami ruwa.”
33
Ya sa mata suna Sheba, domin haka har yau sunan birnin Biyer-sheba.
34
Sa'ad da Isuwa yake da shekara arba'in, ya auro Judit, 'yar Biyeri Bahitte, da Basemat 'yar Elon Bahitte,
35
suka baƙanta wa Ishaku da Rifkatu rai.
← Chapter 25
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 27 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50