bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Genesis 2
Genesis 2
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 1
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 3 →
1
Da haka aka gama yin sama da duniya, da rundunansu.
2
A kwana na bakwai Allah ya gama aikinsa wanda ya yi. Ya kuwa huta a kan kwana na bakwai daga dukan aikinsa da ya yi.
3
Domin haka Allah ya sa wa kwana na bakwai albarka, ya tsarkake shi, don a cikinsa Allah ya huta daga dukan aikin da ya yi na halitta.
4
Waɗannan su ne asalin sama da duniya sa'ad da aka halicce su. A ranar da Ubangiji Allah ya yi duniya da sama,
5
a sa'an nan ba tsire-tsiren saura a duniya, ƙananan ganyayen saura kuma ba su riga sun tsiro ba, gama Ubangiji Allah bai sa a yi ruwa bisa duniya ba tukuna. A lokacin kuwa babu wani wanda zai noma ƙasar,
6
amma sai ƙāsashi yake tasowa daga ƙasa ya shayar da fuskar ƙasa duka.
7
Sa'an nan Ubangiji Allah ya siffata mutum daga turɓayar ƙasa, a cikin kafafen hancinsa kuwa ya hura numfashin rai, mutum kuma ya zama rayayyen taliki.
8
Ubangiji Allah kuwa ya dasa gona a Aidan, wajen gabas, a can ya sa mutumin da ya siffata.
9
Ubangiji Allah ya sa kowane itace mai kyan gani, mai amfani domin abinci, ya tsiro, itacen rai kuwa yana tsakiyar gonar, da kuma itacen sanin nagarta da mugunta.(Far 3.22,24; W. Yah 2.7; 22.2,14,19; Eze 47.12
10
Wani kogi kuma ya malalo daga Aidan ya shayar da gonar, daga nan kuwa ya rarrabu ya zama kogi huɗu.
11
Sunan na fari Fishon, shi ne yake malala kewaye da dukan ƙasar Hawila, inda akwai zinariya.
12
Zinariyar ƙasan nan kuwa kyakkyawa ce. Akwai kuma duwatsu masu daraja a wurin.
13
Sunan kogi na biyu Gihon, shi ne wanda yake malala kewaye da ƙasar Kush.
14
Sunan kogi na uku Taigiris ne, wanda yake malala gabashin Assuriya. Kogi na huɗu kuwa Yufiretis ne.
15
Ubangiji Allah ya ɗauki mutumin ya zaunar da shi cikin gonar Aidan ya noma ta, ya kiyaye ta.
16
Ubangiji Allah ya yi wa mutumin umarni, ya ce, “Kana da 'yanci ka ci daga kowane itace da yake a gonar,
17
amma daga itacen sanin nagarta da mugunta ba za ka ci ba, gama a ranar da ka ci shi za ka mutu lalle.”
18
Sa'an nan sai Ubangiji Allah ya ce, “Bai kyautu mutumin ya zauna shi kaɗai ba, zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.”
19
Haka nan fa, daga cikin ƙasar, Ubangiji ya siffata kowace dabba ta cikin saura da kowane tsuntu na sararin sama, ya kawo su wurin mutumin, ya ga yadda zai kiraye su, duk abin da mutumin ya kirayi mai ran kuwa, sunansa ke nan.
20
Mutumin ya bai wa dabbobi duka suna, da tsuntsayen sararin sama, da kowace irin dabba da take cikin saura, amma ba a sami mataimaki wanda ya dace da mutumin ba.
21
Sai Ubangiji Allah ya sa barci mai nauyi ya kwashe mutumin. Lokacin da yake barci Ubangiji Allah ya cire ɗaya daga cikin haƙarƙarinsa ya cike wurin da nama,
22
haƙarƙarin nan kuwa da Ubangiji Allah ya cire daga mutumin ya yi mace da shi, ya kuwa kawo ta ga mutumin.
23
Sai mutumin ya ce, “Yanzu dai wannan ƙashi ne daga ƙasusuwana, nama ne kuwa daga namana, za a kira ta mace, don daga cikin mutum aka ciro ta.”
24
Domin haka mutum yakan rabu da mahaifinsa da mahaifiyarsa ya kuwa manne wa matarsa, sun zama ɗaya.
25
Da mutumin da matarsa dukansu biyu a tsiraice suke, ba su kuwa ji kunya ba.
← Chapter 1
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 3 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
Recommended Reading
Commentary
Genesis Commentaries
→
Devotional
Genesis Devotional Guide
→
Get This Bible
Hausa Bible (Littafi Mai Tsarki) Study Bible
→