bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Genesis 15
Genesis 15
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 14
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 16 →
1
Bayan waɗannan al'amura, maganar Ubangiji ta zo ga Abram cikin wahayi cewa, “Abram, kada ka ji tsoro, ni ne garkuwarka, kana da lada mai yawa.”
2
Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, me za ka ba ni, ga shi kuwa, ba ni da ɗa? Ko kuwa Eliyezer na Dimashƙu ne zai gāje ni?”
3
Abram kuma ya ce, “Ga shi, ba ka ba ni zuriya ba, ga shi ma wani yaron gidana ne zai gāje ni.”
4
Sai ga maganar Ubangiji ta zo gare shi cewa, “Mutumin nan, ba shi zai gāje ka ba, ɗan cikinka shi zai gāje ka.”
5
Sai Ubangiji ya fito da shi waje ya ce, “Ina so ka dubi sararin sama, ka kuma ƙidaya taurari, in kana iya ƙidaya su.” Sai kuma ya ce masa, “Haka zuriyarka za ta zama.”
6
Ya amince da Ubangiji, Ubangiji kuwa ya lasafta wannan adalci ne a gare shi.
7
Ubangiji kuma ya ce masa, “Ni ne Ubangiji wanda ya fisshe ka daga Ur ta Kaldiyawa, don in ba ka wannan ƙasa ka gāje ta.”
8
Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, yaya zan mallake ta?”
9
Ya ce masa, “Kawo mini karsana bana uku, da burguma bana uku, da rago bana uku, da hazbiya da ɗan tattabara.”
10
Ya kawo masa waɗannan abu duka, ya yanyanka su ya tsattsaga su a tsaka, ya ajiye su gab da juna, amma bai tsaga tsuntsayen a tsaka ba.
11
Sa'ad da tsuntsaye masu cin nama suke sauka bisansu sai Abram ya kore su.
12
Sa'ad da rana take faɗuwa, barci mai nauyi ya kwashe Abram, sai ga babban duhu mai bantsoro ya rufe shi.
13
Ubangiji ya ce wa Abram, “Ka sani lalle ne zuriyarka za ta yi baƙunci cikin ƙasar da ba tata ba ce, za ta kuwa yi bauta, za a kuma tsananta mata har shekara arbaminya,
14
amma zan hukunta al'ummar da suka bauta wa, daga baya kuma da dukiya mai yawa za ta fita.
15
Kai kuwa, cikin salama za ka koma ga iyayenka, da kyakkyawan tsufa za a binne ka.
16
A tsara ta huɗu kuma, zuriyar za ta komo nan, domin adadin muguntar Amoriyawa bai cika ya kai iyaka ba tukuna.”
17
Sa'ad da rana ta fāɗi aka kuwa yi duhu, sai ga tanderun wuta mai hayaƙi da jiniya mai harshen wuta suka ratsa tsakanin abubuwan nan da aka tsattsaga a tsaka.
18
A wannan rana Ubangiji ya yi wa Abram alkawari ya ce, “Ga zuriyarka na ba da wannan ƙasa, daga Kogin Masar zuwa babban kogi, wato Kogin Yufiretis ke nan,
19
ƙasar Keniyawa, da Kenizziyawa, da Kadmoniyawa,
20
da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Refayawa,
21
da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Girgashiyawa, da kuma Yebusiyawa.”
← Chapter 14
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 16 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50