bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Job 12
Job 12
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 11
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 13 →
1
Ayuba ya amsa.
2
“Aha! Ashe, kai ne muryar jama'a, Idan ka mutu hikima ta mutu ke nan tare da kai.
3
Amma ni ma ina da hankali gwargwado, kamar yadda kake da shi, Ban ga yadda ka fi ni ba. Kowa ya san sukan abin da ka faɗa.
4
Har abokaina ma, suna ta yi mini dariya yanzu, Suna ta dariya ko da yake ni adali ne marar laifi, Amma akwai lokacin da Allah ya amsa addu'o'ina.
5
Ba ka shan wahalar kome, duk da haka ka maishe ni abin dariya. Ka bugi mutumin da yake gab da fāɗuwa.
6
Amma ɓarayi da marasa tsoron Allah suna zaune cikin salama, Ko da yake ƙarfinsu ne kaɗai allahnsu.
7
“Don haka tsuntsaye da dabbobi sun fi ka sani, Suna da abu mai yawa da za su koya maka.
8
Ka roƙi talikan da suke a duniya, da cikin teku, hikimar da suke da ita.
9
Dukansu sun sani ikon Ubangiji ne ya yi su.
10
Allah shi ne yake bi da rayukan talikansa. Numfashin dukan mutane kuwa a ikonsa yake.
11
Amma kamar yadda harsunanku suke jin daɗin ɗanɗanar abinci, Haka nan kuma kunnuwanku suke jin daɗin sauraren kalmomi.
12
“Tsofaffi suna da hikima, Amma Allah yana da hikima da iko. Tsofaffi suna da tsinkaya, Amma Allah yana da tsinkaya da ikon aikatawa.
14
Sa'ad da Allah ya rurrushe, wa zai iya sāke ginawa? Wa kuma zai iya fitar da mutumin da Allah ya sa a kurkuku?
15
Akan yi fari sa'ad da Allah ya hana ruwan sama, Rigyawa takan zo sa'ad da ya kwararo ruwa.
16
Allah mai iko ne a kullum kuwa cikin nasara yake Da macuci, da wanda aka cutar, duk ƙarƙashin ikon Allah suke.
17
Yakan mai da hikimar masu mulki wauta, Yakan mai da shugabanni marasa tunani.
18
Yakan tuɓe sarakuna ya sa su kurkuku.
19
Yakan ƙasƙantar da firistoci da mutane masu iko.
20
Yakan rufe bakin waɗanda aka amince da su. Yakan kawar da hikimar tsofaffi.
21
Yakan kunyatar da masu iko, Ya hana wa masu mulki ƙarfi.
22
Yakan aika da haske a wuraren da suke da duhu kamar mutuwa.
23
Yakan sa sauran al'ummai su yi ƙarfi su ƙasaita, Sa'an nan ya fatattaka su, ya hallaka su.
24
Yakan sa shugabanninsu su zama wawaye, Ya bar su su yi ta makuwa, su ruɗe, su ɓata,
25
Su yi ta lalube cikin duhu, su yi ta tangaɗi kamar bugaggu.”
← Chapter 11
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 13 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42