bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Job 21
Job 21
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 20
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 22 →
1
Ayuba ya amsa.
2
“Ku kasa kunne ga abin da nake faɗa, Wannan ita ce ta'aziyyar da nake nema a gare ku.
3
Ku ba ni zarafi in yi magana, sa'an nan in na gama ku amsa in kun ga dama.
4
“Ba da 'yan adam nake faɗa ba, Ina da isasshen hanzarin da zai sa in yi fushi.
5
Ku dube ni, ashe, wannan bai isa ya sa ku yi zuru, Ku firgita, ku yi shiru ba?
6
Sa'ad da na tuna da abin da ya same ni, Sai jikina ya yi suwu, in yi ta makyarkyata ina rawar jiki.
7
Me ya sa Allah yake barin mugaye Har su tsufa su kuma yi arziki?
8
'Ya'yansu da jikokinsu sukan girma a idonsu.
9
Allah bai taɓa aukar wa gidajensu da bala'i ba, Ba su taɓa zama a razane ba.
10
Hakika shanunsu suna ta hayayyafa, Suna haihuwa ba wahala.
11
'Ya'yansu suna guje-guje, Suna tsalle kamar 'yan raguna,
12
Suna rawa ana kaɗa garaya, Ana busa sarewa.
13
Suka yi zamansu da salama, Su mutu shiru ba tare da shan wahala ba.
14
Mugaye sukan ce wa Allah ya ƙyale su kurum, Ba su so su san nufinsa game da hanyoyinsu.
15
Suna tsammani ba amfani a bauta wa Allah, Ko a yi addu'a gare shi domin samun wata fa'ida.
16
Sukan ce ta wurin ƙarfinsu ne suka yi nasara, Amma ban yarda da irin tunaninsu ba.
17
“An taɓa kashe hasken mugun mutum? Ko masifa ta taɓa fāɗa wa wani daga cikinsu? Allah ya taɓa hukunta wa mugu da fushi,
18
Ya kuma sa su zama kamar tattakar da iska yake kwashewa? Ko kuma kamar ƙura wadda hadiri yake kwashewa?
19
“Kukan ce Allah yakan hukunta yaro saboda zunuban mahaifinsa. A'a! Allah dai yakan hukunta wa masu zunubi. Ya kuma nuna ya yi haka saboda zunubansu ne.
20
Bari dai a hukunta masu zunubi Su kuma ga hasalar Allah.
21
Bayan rasuwar mutum, Ruwansa ne ya sani ko 'ya'yansa suna jin daɗi?
22
Mutum zai iya koya wa Allah? Mutum zai iya shara'anta wa Allah Mai Iko Dukka?
23
“Waɗansu mutane sukan yi zamansu ba ciwon kome har ranar mutuwarsu, Suna cikin farin ciki da jin daɗi,
24
Jikunansu kuwa sun yi ɓulɓul.
25
Waɗansu kuwa ba su taɓa sanin farin ciki ba. Sukan yi dukan kwanakinsu su mutu da baƙin ciki.
26
Amma duk abu guda ne su, mutuwa za su yi, a binne, Tsutsotsi su lulluɓe su duka.
27
“Na san irin tunaninku na hassada,
28
Kuna ta tambaya, ‘Ina ne gidan babban mutumin nan yanzu, Wato mutumin da yake aikata mugunta?’
29
“Ashe, ba ku yi magana da matafiya ba? Ba ku kuma san rahoton da suka kawo ba?
30
A ranar da Allah ya yi fushi, ya yi hukunci, A kullum mugun ne kaɗai yakan kuɓuta.
31
Ba wanda zai fito fili ya zargi mugun, Ko ya mayar masa da martani.
32
Sa'ad da aka ɗauke shi zuwa hurumi, A inda ake tsaron kabarinsa,
33
Dubban mutane sukan tafi wurin jana'izarsa, Akan mai da ƙasa a kan gawarsa a hankali.
34
“Amma ku, ƙoƙari kuke yi ku ta'azantar da ni da maganganun banza. Duk abinda kuka faɗa ƙarya ne!”
← Chapter 20
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 22 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42