bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Job 4
Job 4
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 3
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 5 →
1
Elifaz ya yi magana.
2
“Ayuba, za ka ji haushi in na yi magana? Ba zan iya kannewa, in yi shiru ba.
3
Ka koya wa mutane da yawa, Ka kuma ƙarfafa hannuwan marasa ƙarfi.
4
Idan wani ya yi tuntuɓe, Ya gaji, ya rasa ƙarfi, Kalmominka suka ƙarfafa zuciyarsa, Har ya iya tsayawa kyam.
5
Yanzu naka lokacin wahala ya zo, Kai kuwa ka rikice, ka kasa ɗaurewa,
6
Kana yi wa Allah sujada, Ba wani laifi a zamanka, Ya kamata ka amince ka sa zuciya.
7
“Yanzu fa sai ka yi tunani. Ka faɗi bala'i ɗaya wanda ya taɓa fāɗa wa adalin mutum.
8
Na taɓa ganin mutane suna huɗe gonar mugunta, Suna shuka mugunta, Suka kuwa girbe mugunta.
9
A cikin fushinsa Allah yakan hallaka su kamar hadiri.
10
Mugaye sukan yi ruri suna gurnani kamar zakoki, Amma Allah yakan sa su yi tsit, Ya kakkarya haƙoransu.
11
Kamar zakoki da ba su da abin da za su kashe su ci, Haka nan za su mutu, 'ya'yansu kuwa su warwatse duka.
12
“Wata rana wani saƙo ya zo a hankali, Har da ƙyar nake iya ji,
13
Kamar wani irin mafarki mai razanarwa yake, Wanda ya hana ni jin daɗin barcina.
14
Na yi rawar jiki ina makyarkyata, Duk jikina yana ta ɓare-ɓare don tsoro.
15
Wata iska marar ƙarfi ta taɓa fuskata, Sai fatar jikina ta yanƙwane saboda fargaba.
16
Na ga wani abu can yana tsaye, Na zura ido, amma ban san kowane irin abu ba ne, Ina cikin wannan hali sai na ji murya,
17
Ta ce, ‘Mutum yana iya zama adali a gaban Allah? Akwai kuma wanda yake mai tsarki a gaban Mahaliccinsa?
18
Allah ba ya amince wa barorinsa na cikin sammai, Yakan sami laifi a wurin mala'ikunsa.
19
Ta ƙaƙa zai amince da talikinsa wanda aka yi da ƙasa, Abin da yake na ƙura, ana kuwa iya murƙushe shi kamar asu.
20
Mai yiwuwa ne mutum yana raye da safe Amma ya mutu ba a sani ba kafin maraice.
21
Duk abin da ya mallaka an ɗauke, Duk da haka ya mutu cikin rashin hikima.’ ”
← Chapter 3
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 5 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42