bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Job 38
Job 38
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 37
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 39 →
1
Ubangiji ya yi magana da Ayuba ta cikin guguwa.
2
“Wane ne wannan da yake ɓāta shawara Da maganganu marasa ma'ana?
3
Ka tashi tsaye ka sha ɗamara kamar namiji, Zan yi maka tambaya, kai kuwa ka ba ni amsa.
4
A ina kake sa'ad da na aza harsashin gina duniya? Faɗa mini idan ka sani.
5
Wane ne ya zayyana kusurwoyinta? Hakika ka sani. Wane ne kuma ya auna ta?
6
A kan me aka kafa tushenta? Wa ya aza dutsen kan kusurwarta?
7
Sa'ad da taurarin asuba suka raira waƙa tare, Sai mala'iku duka suka yi sowa saboda murna.
8
“Wa ya yi wa teku iyaka Sa'ad da ta tumbatso daga zurfafa?
9
Sa'ad da na suturta ta da gizagizai, Na yi mata maɗauri da duhu ƙirin.
10
Na sa mata iyakoki, Na sa mata ƙyamare da ƙofofi,
11
Na ce mata, ‘Iyakar inda za ki tsaya ke nan, Ba za ki wuce ba. Nan raƙuman ruwanki masu tumbatsa za su tsaya.’
12
“Ayuba, a dukan kwanakinka Ka taɓa umartar wayewar gari, Ko ka sa alfijir ya keto?
13
Da gari ya waye, Ka kawar da muguntar da ake yi da dare?
14
Yakan sāke kamar lakar da take ƙarƙashin hatimi, Yakan rine kamar riga.
15
Akan hana wa mugaye haske, Sa'ad da sukan ɗaga hannuwansu sama akan kakkarya su.
16
“Ko ka taɓa shiga cikin maɓuɓɓugan teku? Ka taɓa yin tafiya a cikin zurfin lallokin teku?
17
An taɓa nuna maka ƙofofin mutuwa? Ko kuwa ka taɓa ganin ƙofofin duhu ƙirin?
18
Ko ka san iyakar fāɗin duniya? Ka amsa mini in ka san dukan waɗannan.
19
“Ina hanya zuwa wurin da haske yake? A ina kuma duhu yake?
20
Ka san iyakarsa ko mafarinsa?
21
Ka sani, gama a lokacin nan an haife ka, Shekarunka kuwa suna da yawa.
22
“Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara? Ko kuwa ka taɓa shiga rumbunan ajiyar ƙanƙara?
23
Na adana su ne don lokacin wahala, Domin ranar faɗa da ta yaƙi.
24
Ina hanya zuwa inda rana take fitowa, Ko kuma ta inda iskar gabas take hurowa ta māmaye ko'ina?
25
“Wa ya haƙa hanyar da ruwan sama mai kwararowa zai bi? Da kuma hanyar da gatarin aradu zai bi?
26
Wa ya kuma kawo ruwan sama a ƙasar da ba mutane, Da a cikin hamada inda ba kowa,
27
Don a shayar da zozayar ƙasa inda ba kowa, Har ta tsiro da ciyayi?
28
“Ruwan sama yana da mahaifi? Wa ya haifi ɗiɗɗigar raɓa?
29
Wace ce mahaifiyar ƙanƙara? Wace ce kuma ta haifi jaura?
30
Ruwa ya daskare ya yi ƙarfi kamar dutse, Teku ta daskare.
31
“Za ka iya ɗaure sarƙoƙin kaza-da-'ya'yanta? Ko ka iya kwance igiyoyin mafarauci-da-kare-da-zomo?
32
Za ka iya bi da yaneyanen sararin sama bisa ga fasalinsu?
33
Ka san ka'idodin sammai? Ko ka iya faɗar yadda suka danganta da duniya?
34
“Kana iya yi wa gizagizai tsawa, Don su kwararo ruwan sama, ya rufe ka?
35
Ka iya aikar walƙiyoyi su tafi, Sa'an nan su ce maka, ‘Ga mu mun zo?’
36
Wa ya sa hikima a gizagizai, Ko kuma wa ya ba da ganewa ga kāsashi?
37
Akwai mai hikimar da zai iya ƙidaya gizagizai? Ko kuwa wa zai iya karkato da salkunan ruwan sammai,
38
Sa'ad da ƙura ta murtuke ta taru jingim, ta game kam?
39
“Ka iya farauto wa zakoki abinci? Ko ka ƙosar da yunwar sagarun zakoki,
40
Sa'ad da suke fako a kogwanninsu, Ko suna kwance suna jira a maɓoyarsu?
41
Wa yake tanada wa hankaka abincinsa, Sa'ad da 'ya'yansa suke kuka ga Allah, Suna kai da kawowa saboda rashin abinci?”
← Chapter 37
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 39 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42