bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Job 16
Job 16
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 15
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 17 →
1
Ayuba ya yi magana.
2
“Ai, na taɓa jin magana irin wannan, Ta'aziyyar da kake yi azaba ce kawai.
3
Ka dinga yin magana ke nan har abada? A kullum maganarka ita ce dahir?
4
In da a ce a matsayina kake, ni kuma ina a naka, Ina iya faɗar duk abin da kake faɗa yanzu. Da sai in kaɗa kaina da hikima, In dulmuyar da kai a cikin rigyawar maganganu.
5
Da sai in ba ka shawara ta ƙarfafawa, In yi ta yi maka maganar ta'azantarwa.
6
“Amma ba abin da zan faɗa wanda zai taimaka, Yin shiru kuma ba zai raba ni da azaba ba.
7
Ka gajiyar da ni, ya Allah, Ka shafe iyalina.
8
Ka kama ni, kai maƙiyina ne. Na zama daga fata sai ƙasusuwa, Mutane suka ɗauka, cewa wannan ya tabbatar ni mai laifi ne.
9
Allah ya kakkarya gaɓoɓina da fushinsa, Yana dubana da ƙiyayya.
10
Mutane sun buɗe baki don su haɗiye ni Suna kewaye ni suna ta marina.
11
Allah ya bashe ni ga mugaye.
12
Dā ina zamana da salama, Amma Allah ya maƙare ni, Ya fyaɗa ni ƙasa ya ragargaza ni. Allah ya maishe ni abin bārata.
13
Ya harbe ni da kibau daga kowane gefe. Kiban sun ratsa jikina sun yi mini rauni, Duk da haka bai nuna tausayi ba!
14
Ya yi ta yi mini rauni a kai a kai, Ya fāɗa mini kamar soja da ƙiyayya ta haukata.
15
“Ina makoki saye da tsummoki, Ina zaune cikin ƙura a kunyace.
16
Na yi ta kuka har fuskata ta zama ja wur, Idanuna kuma suka yi luhuluhu.
17
Amma ban yi wani aikin kama-karya ba, Addu'ata ga Allah kuwa ta gaskiya ce.
18
“Duniya, kada ki ɓoye laifofin da aka yi mini! Kada ki yi shiru da roƙon da nake yi na neman adalci!
19
Akwai wani a Sama Wanda zai tsaya mini ya goyi bayana.
20
Ina so Allah ya ga hawayena, Ya kuma ji addu'ata.
21
“Ina so wanda zai yi roƙo ga Allah domina, Kamar yadda mutum yakan yi roƙo domin abokinsa.
22
Yanzu shekaruna wucewa suke yi, Ina bin hanyar da ba a komawa.”
← Chapter 15
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 17 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42