bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Job 30
Job 30
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 29
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 31 →
1
“Amma yanzu waɗanda na girme su, sai ba'a suke mini, Waɗanda iyayensu maza ba su fi karnukan da suke kiwon garken tumakina ba.
2
Wace riba zan samu ta wurin ƙarfin hannuwansu waɗanda ba su da sauran kuzari?
3
Saboda rashi da matsananciyar yunwa sun rame, Sai gaigayar ƙasa suke yi da dare, a cikin kufai.
4
Sukan tsinki ganyaye masu ɗaci na jeji su ci, Sukan ci doyar jeji.
5
Aka kore su daga cikin mutane, Suka yi ta binsu da ihu kamar yadda ake yi wa ɓarawo,
6
Sai a kwazazzabai suke zama Da a ramummuka da kogwannin duwatsu.
7
Suka yi ta kuka a jeji, Suka taru wuri ɗaya a cikin sarƙaƙƙiya.
8
Mutane ne marasa hankali marasa suna! Aka kore su daga ƙasar.
9
“Yanzu na zama abin waƙa gare su, Abin ba'a kuma a gare su.
10
Suna ƙyamata, guduna suke yi, Da ganina, sai su tofa mini yau.
11
Domin Allah ya katse lakata, ya ƙasƙanta ni, Saboda haka sun raba ni da zuriyata,
12
A hannun dama 'yan tā da zaune tsaye sun taso mini, Sun runtume ni, sun tura ni a hanyarsu ta hallakarwa.
13
Sun datse hanyata, Sun jawo mini bala'i, Ba kuwa wanda ya hana su.
14
Sun kutsa kamar waɗanda suka karya doka, Sun auka mini da dukan ƙarfinsu kamar yadda suka yi nufi.
15
Sun firgita ni, Sun kori darajata kamar da iska, Wadatata kuma ta shuɗe kamar girgije.
16
“Yanzu zuciyata ta narke Kwanakin wahala sun same ni.
17
Da dare ƙasusuwana karkaɗuwa suke, Azaba tana ta gaigayata ba hutawa.
18
An yi mini kamun kama-karya, An ci wuyan rigata.
19
Allah ya jefar da ni cikin laka, Na zama kamar ƙura ko toka,
20
“Na yi kira gare ka, ya Allah, amma ba ka amsa mini ba, Na yi addu'a kuma, amma ba ka kula da ni ba.
21
Ka zama mugu a gare ni, Da ƙarfin dantsenka ka tsananta mini.
22
Ka jefa ni cikin guguwa, ka sa ni in hau ta, Ka yi ta shillo da ni cikin rugugin hadiri.
23
Hakika na sani za ka kai ni ga mutuwa, Gidan da aka ƙaddara wa kowane mai rai.
24
“Ashe, wanda yake gab da gagarumar hallaka, Ba zai miƙa hannu ya roƙi taimako a masifar da yake sha ba?
25
Ashe, ban yi kuka saboda wanda yake shan wahala ba? Ashe, ban yi ɓacin rai saboda matalauta ba?
26
Amma sa'ad da na sa zuciya ga alheri, sai ga mugunta, Sa'ad da nake jiran haske, sai ga duhu ya zo.
27
Zuciyata tana tafasa, ba ta kwanciya, Kwanakin wahala sun auko mini.
28
Na yanƙwane, amma ba yanƙwanewar rana ba, Na tsaya a gaban taron jama'a, ina roƙon taimako.
29
“Na zama ɗan'uwan dila, Na kuma zama aminin jiminai.
30
Fatata ta takura, ta zama baƙa, Ƙasusuwana suna zogi saboda zafi,
31
Saboda haka garayata ta zama ta makoki, Sarewata kuma ta zama muryar masu kuka.”
← Chapter 29
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 31 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42