bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Isaiah 16
Isaiah 16
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 15
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 17 →
1
Daga birnin Sela a hamada, mutanen Mowab za su aiko da kaiwar rago ga mai mulki a Urushalima.
2
Za su dakata a gaɓar kogin Arnon, za su yi ta kai da kawowa kamar tsuntsayen da aka kora daga sheƙunansu.
3
Suna ce wa mutanen Yahuza, “Ku faɗa mana abin da za mu yi. Ku kāre mu, ku bar mu mu huta a inuwarku mai sanyi kamar inuwar itace da tsakar rana. Mu 'yan gudun hijira ne, ku ɓoye mu inda ba wanda zai gan mu.
4
Ku bar mu mu zauna ƙasarku. Ku kāre mu daga masu neman hallaka mu.” Zalunci da hallakarwa za su ƙare, masu lalatar da ƙasar za su ƙare.
5
Sa'an nan wani daga cikin zuriyar Dawuda zai zama sarki. Zai mallaki jama'a da aminci da ƙauna. Zai aikata abin da yake daidai da hanzari, zai sa a aikata adalci.
6
Mutanen Yahuza sun ce, “Mun ji irin fāriyar da mutanen Mowab suke yi. Mun sani su masu girmankai ne, masu ruba, amma fankamarsu ta banza ce.”
7
Mutanen Mowab za su yi kuka saboda wahalar da suke sha. Dukansu za su yi kuka sa'ad da suka tuna da kyakkyawan abincin da suka riƙa ci a birnin Kir-hareset. Za a kore su har su fid da zuciya.
8
Gonakin da suke kusa da Heshbon, da gonakin inabin da suke Sibma an lalatar da su, gonakin inabin nan waɗanda ruwan inabinsu suke sa masu mulkin al'ummai su bugu. Da kurangunsu sun taɓa yaɗuwa zuwa gabas har suka kai birnin Yazar da cikin hamada, wajen yamma kuma sai da suka dangana da gefen Tekun Gishiri.
9
Yanzu ina kuka saboda gonakin inabin Sibma kamar yadda na yi wa na Yazar. Na zub da hawayena saboda Heshbon da Eleyale, domin ba a sami kaka mai albarka ba, wadda za ta sa mutane yin murna.
10
Ba wanda yake farin ciki a cikin sauruka masu dausayi. Ba wanda yake sowa ko waƙa a cikin gonakin inabi. Ba mai matse ruwan inabi, sowar murna ta ƙare.
11
Na yi nishi da ɓacin zuciya a kan Mowab, na yi nishi da baƙin ciki saboda Kir-heres.
12
Mutanen Mowab sun gajiyar da kansu da zuwa wurin matsafarsu na kan dutse da masujadarsu, suna addu'a, amma ba zai amfana musu kome ba.
13
Wannan shi ne jawabin da Ubangiji ya riga ya yi a kan Mowab.
14
Yanzu Ubangiji ya ce, “A shekara uku daidai, dukiyar Mowab mai yawan nan za ta ƙare. Daga cikin ɗumbun mutanenta 'yan kaɗan ne kaɗai za su ragu, za su kuma zama marasa ƙarfi.”
← Chapter 15
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 17 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64
65
66