bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Isaiah 44
Isaiah 44
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 43
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 45 →
1
Ubangiji ya ce, “Ka saurara yanzu, ya Isra'ila, bawana, Zaɓaɓɓun mutanena, zuriyar Yakubu,
2
Ni ne Ubangiji wanda ya halicce ku, Tun farko, na taimake ku. Kada ku ji tsoro, ku bayina ne, Zaɓaɓɓun mutanena waɗanda nake ƙaunarsu.
3
“Zan ba da ruwa ga ƙasa mai ƙishi, In kuma sa rafuffuka su yi gudu a hamada. Zan kwararo da albarka a kan 'ya'yanku, In sa albarkata kuma a kan zuriyarku.
4
Za su yi kumari kamar ciyawar da ta sami ruwa sosai, Kamar itatuwan wardi a gefen rafuffukan ruwa mai gudu.
5
“Da ɗaya ɗaya da ɗaya ɗaya mutane za su ce, ‘Ni na Ubangiji ne!’ Za su zo su haɗa kai da jama'ar Isra'ila. Ko wanne zai ɗaura sunan Ubangiji a dantsensa, Ya ce da kansa ɗaya daga cikin mutanen Allah.”
6
Ubangiji, wanda yake mulkin Isra'ila, ya kuma fanshe su, Ubangiji Mai Runduna, yake faɗar wannan, “Ni ne farko, da ƙarshe, Allah Makaɗaici, Ba wani Allah sai ni.
7
Ko akwai wanda zai iya yin abin da na yi, Ya kuma fito fili ya faɗi abin da zai faru Tun daga farko, har zuwa ƙarshe?
8
Ya jama'ata, kada ku ji tsoro! Kun sani tun daga zamanin dā can, har zuwa yanzu, Na faɗa tun da wuri abin da zai faru. Ku ne kuwa shaiduna! Ko akwai wani Allah? Ko akwai wani Allah mai iko da ban taɓa jin labarinsa ba?”
9
Dukan waɗanda suke ƙera gumaka mutanen banza ne, gumakan da suke sa wa kuɗi da tsada kuma aikin banza ne. Waɗanda suke yi wa gumaka sujada kuwa makafi ne su, jahilai, za su sha kunya.
10
Wannan aikin banza ne, mutum ya yi siffa da ƙarfe don ya yi mata sujada!
11
Dukan wanda ya yi mata sujada za a ƙasƙantar da shi. Mutanen da suka ƙera gumakan, 'yan adam ne, ba wani abu ba. Bari su zo su tsaya gaban shari'a, za su razana, su kuma sha kunya.
12
Maƙeri yakan ɗauki guntun ƙarfe ya sa shi a wuta ya yi aiki. Da hannunsa mai ƙarfi yana ɗaukar guduma yana bugun ƙarfen, yana mai da shi siffa. Yakan ji yunwa, da ƙishi, yakan kuma ji gajiya.
13
Masassaƙi yakan auna itace. Ya zana siffa da alli, sa'an nan ya sassaƙe shi da kayan aikinsa. Ya yi shi da siffar mutum kyakkyawa, domin a ajiye shi a masujadarsu.
14
Zai yiwu ya sare itacen al'ul ya yi da shi, ko kuwa ya zaɓi itacen oak, ko na kasharina daga jeji. Ko kuwa ya dasa wani itace, ya jira ruwan sama don ya sa itacen ya yi girma.
15
Mutum yakan yi abin wuta da wani sashi na itacen, wani sashi kuma ya yi gunki da shi. Yakan hura wuta da wani sashi don ya ji ɗumi, yakan kuma toya gurasa. Yakan yi gunki da wani sashi, ya riƙa yi masa sujada!
16
Yakan hura wuta da wani sashi domin ya gasa nama, ya ci, ya ƙoshi. Ya ji ɗumi ya ce, “Kai, ɗumi da daɗi, wutar tana da kyau!”
17
Sauran itacen ya mai da shi gunki. Yana rusunawa ya yi masa sujada. Yana addu'a gare shi yana cewa, “Kai ne Allahna, ka cece ni!”
18
Irin waɗannan mutane dakikai ne, har ba su san abin da suke yi ba. Sun rufe idanunsu da tunaninsu ga gaskiya.
19
Masu ƙera gumaka ba su da ko tunanin da za su ce, “Na ƙone wani sashi na itacen nan. Na toya gurasa a garwashin, na kuma gasa nama, na ci shi, na kuwa ce sauran itacen zan sassaƙa gunki da shi. Ga ni yanzu, ina ta rusunawa gaban guntun itace!”
20
Ya zama daidai kamar mutum ya ci toka. Manufarsa ta wauta ta ɓatar da shi, har ba yadda za a iya taimakonsa. Ba zai iya ganewa ba, gunkin da ya riƙe a hannunsa ba allah ba ne ko kaɗan.
21
Ubangiji ya ce, “Ka tuna da waɗannan abu, ya Isra'ila, Ka tuna kai bawana ne. Na halicce ka domin ka zama bawana, Ba zan taɓa mantawa da kai ba.
22
Na shafe zunubanka kamar baƙin girgije, Da girgije kuma zan rufe laifofinka Ka komo wurina, ni ne na fanshe ka.”
23
Ku yi sowa ta farin ciki ya ku sammai! Ku yi sowa ku zurfafan wurare na duniya! Ku yi sowa ta murna, ku duwatsu, da kowane itace na jeji! Ubangiji ya fanshi mutanensa, Isra'ila, Saboda haka ya nuna girmansa.
24
“Ni ne Ubangiji, Mahaliccinku, Mai Fansarku. Ni ne Ubangiji, Mahaliccin dukkan abu. Ni kaɗai na shimfiɗa sammai, Ba wanda ya taimake ni sa'ad da na yi duniya.
25
Na sa masu duba su zama wawaye, Na sassāke annabce-annabcen masanan taurari. Na bayyana kuskuren maganar masu hikima, Na kuma nuna masu hikimarsu wauta ce.
26
Amma sa'ad da bawana ya yi annabci, Sa'ad da na aika da manzona domin ya bayyana shirye-shiryena, Na sa waɗannan shirye-shirye da annabce-annabce su cika. Ina faɗa wa Urushalima, cewa mutane za su sāke zauna a can, Za a kuma sāke gina biranen Yahuza. Waɗannan birane za su daina zama kufai.
27
Na yi umarni na sa teku ta ƙafe.
28
Na ce wa Sairus, ‘Kai ne wanda za ka yi mulki domina, Za ka yi abin da nake so ka yi, Za ka ba da umarni, cewa a sāke gina Urushalima, A kuma kafa harsashin ginin Haikali.’ ”
← Chapter 43
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 45 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64
65
66