bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Isaiah 42
Isaiah 42
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 41
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 43 →
1
Ubangiji ya ce, “Ga bawana, wanda na ƙarfafa, Wanda na zaɓa, wanda nake jin daɗinsa. Na cika shi da ikona, Zai kuwa kawo shari'ar gaskiya ga dukan al'ummai.
2
Ba zai yi tsawa ko ya ta da muryarsa ba, Ko ya yi jawabi da babbar murya a tituna.
3
Zai lallaɓi marasa ƙarfi, Ya nuna alheri ga tafkakku. Zai kawo madawwamiyar gaskiya ga duka.
4
Ba zai fid da zuciya ko ya karai ba, Zai kuma kafa gaskiya a duniya, Manisantan ƙasashe sun zaƙu, suna jiran koyarwarsa.”
5
Allah ya halicci sammai ya kuma shimfiɗa su, Ya yi duniya, da dukan masu rai nata, Ya ba da rai da numfashi ga dukan mutanenta. Yanzu kuwa Ubangiji Allah ya ce wa bawansa,
6
“Ni Ubangiji, na kira ka, na kuma ba ka iko Domin ka ga ana aikata gaskiya a duniya. Ta wurinka zan yi wa dukan mutane alkawari, Ta wurinka zan kawo haske ga al'ummai.
7
Za ka buɗe idanun makafi, Ka kuma kwance waɗanda suke ɗaure a kurkuku masu duhu.
8
“Ni kaɗai ne Ubangiji Allahnka. Ba wani allahn da zai sami ɗaukakata, Ba zan bar gumaka su sami yabona ba.
9
Abubuwan da na faɗa yanzu sun cika. Yanzu zan faɗa muku sababbin abubuwa, Tun kafin ma su soma faruwa.”
10
Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji, Ku raira yabo ku dukan duniya! Ku yabe shi, ku da kuke tafiya ta teku, Ku yabe shi, ku dukan halitta a teku! Ku raira, ku manisantan ƙasashe, da dukan waɗanda suke a can!
11
Bari hamada da garuruwanta su yabi Allah, Bari mutanen Kedar su yabe shi! Bari su da suke zaune a birnin Sela Su yi sowa don murna daga ƙwanƙolin duwatsu!
12
Bari waɗanda suke a manisantan ƙasashe su yi yabo, Su kuma girmama Ubangiji!
13
Ubangiji ya fita domin ya yi yaƙi kamar jarumi, Ya shirya, ya kuma ƙosa domin yaƙi. Ya yi gunzar yaƙi da tsawar yaƙi, Ya nuna ikonsa a kan abokan gābansa.
14
Allah ya ce, “Na daɗe na yi shiru, Ban amsa wa jama'ata ba. Amma yanzu lokaci ya yi da zan yi wani abu, Na yi ƙara kamar matar da take fama da zafin naƙuda.
15
Zan lalatar da tuddai da duwatsu, In kuma busar da ciyawa da itatuwa, Zan mai da kwaruruka inda akwai rafi hamada, In kuma busar da kududdufan ruwa.
16
“Zan yi wa mutanena makafi jagora A hanyar da ba su taɓa bi ba. Zan sa duhunsu ya zama haske, In kuma sa ƙasa mai kururrumai ta zama sumul a gabansu. Ba zan kasa yin waɗannan abu ba.
17
Dukan waɗanda suke dogara ga gumaka, Masu kiran siffofi allolinsu, Za a ƙasƙantar da su, su kuma sha kunya.”
18
Ubangiji ya ce, “Ku kasa kunne, ya ku kurame! Ku duba da kyau sosai, ku makafi!
19
Akwai sauran wanda ya fi bawana makanta, Ko wanda ya fi manzona kurunta, wato wanda na aiko?
20
Isra'ila, kun ga abu da yawa, Amma bai zama da ma'ana a gare ku ba ko kaɗan. Kuna da kunnuwan da za ku ji, Amma a ainihi me kuka ji?”
21
Ubangiji shi Allah ne da ya ƙosa ya yi ceto saboda gaskiyarsa, Saboda haka yana so a girmama koyarwarsa,
22
Amma yanzu an washe mutanensa, Aka kukkulle su a kurkuku, Aka ɓoye su a rami. Aka yi musu fashi, aka washe su, Ba wanda ya zo domin ya kuɓutar da su.
23
Ko akwai wanda zai kasa kunne ga wannan? Ko za ku kasa kunne ku yi lura daga yanzu?
24
Wane ne ya ba da Isra'ila ga masu waso? Ubangiji ne kansa, shi wanda muka yi wa zunubi! Ba mu iya zama kamar yadda yake so mu yi ba, Ko mu yi biyayya da koyarwarsa da ya ba mu.
25
Domin haka ya sa mu ji zafin fushinsa, Mu kuma sha wahalar da yaƙi ya kawo. Fushinsa ya yi ƙuna cikin dukan Isra'ila kamar wuta, Amma ba mu taɓa sanin abin da yake faruwa ba, Ba mu koyi kome daga wannan ba ko kaɗan.
← Chapter 41
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 43 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64
65
66