bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Isaiah 26
Isaiah 26
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 25
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 27 →
1
Rana tana zuwa da jama'a za su raira wannan waƙa a ƙasar Yahuza. Birni ƙaƙƙarfa ne, Allah kansa yake tsare garukansa!
2
A buɗe ƙofofin birnin, A bar amintacciyar al'umma ta shiga, Al'ummar da jama'arta take aikata abin da yake daidai.
3
Kai kake ba da cikakkiyar salama, ya Ubangiji, Ga waɗanda suke riƙe da manufarsu da ƙarfi, Waɗanda suke dogara gare ka.
4
Ku dogara ga Ubangiji har abada. Zai kiyaye mu kullayaumin.
5
Ya ƙasƙantar da masu girmankai, Ya hallaka ƙaƙƙarfan birnin da suke zaune ciki, Ya rusa garunsa ƙasa.
6
Waɗanda aka zalunta, a kansa suke tafiya yanzu, Suna tattaka shi da ƙafafunsu.
7
Ka sa hanyar mutanen kirki ta yi sumul, Hanyar da suke bi ta yi bai ɗaya,
8
Muna bin nufinka, muna sa zuciya gare ka. Kai kaɗai ne bukatarmu.
9
Da dare ina zuba ido gare ka da zuciya ɗaya. Sa'ad da kake yi wa duniya da jama'arta shari'a Dukansu za su san yadda adalci yake.
10
Ko da yake kana yi wa mugaye alheri, Duk da haka ba su taɓa koyon abin da yake na kirki ba. Har a nan ma, a ƙasar adalai, Suna ta aikata kuskure, Sun ƙi ganin girmanka.
11
Maƙiyanka ba su san za ka hukunta su ba. Ya Ubangiji, ka kunyatar da su, ka sa su sha wahala, Wato su sha wahalar hukuncin da ka shirya. Ka nuna musu yawan ƙaunar da kake yi wa jama'arka.
12
Kai za ka wadata mu, ya Ubangiji, Duk abin da muka iya yi daga gare ka ne.
13
Ya Ubangiji Allahnmu, waɗansu sun mallake mu, Amma kai kaɗai ne Ubangijinmu.
14
Yanzu kuwa sun mutu, ba za su ƙara rayuwa ba, Kurwarsu ba za ta tashi ba, Domin ka hukunta su, ka hallaka su. Ba wanda zai ƙara tunawa da su.
15
Ya Ubangiji, ka sa al'ummarmu ta yi ƙarfi, Ka faɗaɗa karkararta a kowane gefe, Wannan kuwa ya sa ana girmama ka.
16
Ka hukunta jama'arka, ya Ubangiji, A cikin azaba sun yi addu'a gare ka.
17
Kai ne, ya Ubangiji, ka sa muka yi kuka, Kamar macen da take naƙuda tana kuka da azaba.
18
Muna shan azaba da wahala, Amma ba abin da muka haifa. Ba mu ciwo wa ƙasarmu nasara ba, Ba abin da muka kammala!
19
Mutanenmu da suka mutu za su sāke rayuwa! Jikunansu za su sāke rayuwa! Dukan waɗanda suke kwance cikin kaburburansu Za su farka, su yi waƙa don farin ciki! Kamar laimar raɓa wanda yake wartsakar da duniya, Haka Ubangiji zai rayar da waɗanda suka daɗe da mutuwa.
20
Jama'ata, ku shiga gidajenku, ku kukkulle ƙofofi, ku ɓoye kanku ɗan lokaci, kafin Allah ya huce daga fushinsa.
21
Ubangiji yana zuwa ya hukunta jama'arsa a duniya saboda zunubansu. Kashe-kashen da aka yi a duniya a ɓoye, za a bayyana su, ƙasa ba za ta ƙara ɓoye waɗanda aka kashe ba.
← Chapter 25
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 27 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64
65
66