bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Isaiah 48
Isaiah 48
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 47
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 49 →
1
Ku kasa kunne, ya jama'ar Isra'ila, Ku da kuke zuriyar Yahuza. Kuna rantsuwa da sunan Ubangiji, Kuna nuna kamar kuna sujada ga Allah na Isra'ila, Amma abin da kuke faɗa ba haka kuke nufi ba.
2
Amma duk da haka kuna fāriya, da cewa Ku ne mazaunan birni mai tsarki, Kuna kuma dogara ga Allah na Isra'ila, Wanda sunansa Ubangiji, Mai Runduna.
3
Ubangiji ya ce wa Isra'ila, “Tuntuni na yi faɗi a kan abin da zai faru, Sa'an nan na sa ya faru ba labari!
4
Na sani kuna nuna ku masu taurinkai ne, Kuna ƙage kamar ƙarfe, kun taurare kamar tagulla.
5
Tuntuni na yi faɗi a kan makomarku, Na hurta abubuwa tun kafin su faru, Domin kada ku ɗauka cewa gumakanku ne suka yi su, Siffofinku ne kuma suka sa abin ya zama haka.
6
“Dukan abin da na faɗa yana cika yanzu, Sai ku yarda, faɗata gaskiya ce. Yanzu zan faɗa muku sababbin abubuwan da za su zo, Abubuwan da ban bayyana su a dā ba.
7
Yanzu ne kaɗai nake sawa su faru, Ba wani abu makamancin wannan da ya faru a baya. Da ya faru, da za ku ɗauka cewa kun san kome a kansa.
8
Na sani ba za a iya gaskata ku ba, Tun daga haihuwarku kuma an san ku da tayarwa. Shi ya sa ba ku taɓa jin wannan ba ko kaɗan, Ko kalma ɗaya ba ta taɓa shiga kunnenku ba.
9
“Saboda mutane su yi yabon sunana Shi ya sa nake danne fushina, Ina kuma ɓoye shi, kada in hallaka ku.
10
Na gwada ku da wutar wahala, Kamar yadda ake tace azurfa a tanda, Amma na tarar ba ku da amfani.
11
Abin da na yi, na yi shi don kaina ne, Ba zan bari a rasa girmama sunana ba, Ko kuwa wani dabam ya sami ɗaukaka Wadda take tawa ce, ni kaɗai.”
12
“Ku kasa kunne gare ni, ya Isra'ila, jama'ar da na kira! Ni ne Allah, farko, da ƙarshe, Allah Makaɗaici!
13
Dantsena ne ya kafa harsashin ginin duniya, Ya kuma shimfiɗa sammai. Lokacin da na kira duniya da sararin sama, Sukan zo nan da nan, su gabatar da kansu!
14
“Ku tattaru, ku duka, ku kasa kunne! Ba ko ɗaya cikin alloli da zai iya yin annabci ba, Cewa mutumin da na zaɓa, shi zai iya fāɗa wa Babila, Zai yi abin da na umarce shi.
15
Ni ne na yi magana, na kuwa kira shi, Na yi masa jagora na kuwa ba shi nasara.
16
“Yanzu fa, sai ku matso kusa da ni, Ku ji abin da nake faɗa. Tun da farko na yi magana da ku a fili, A koyaushe nakan cika maganata.” (Yanzu Ubangiji Allah ya ba ni iko, ya kuwa aike ni.)
17
Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Ubangiji, wanda ya fanshe ku, ya ce, “Ni ne Ubangiji Allahnku, Wanda yake so ya koya muku domin amfanin kanku, Ya kuwa nuna muku hanyar da za ku bi.
18
“Da ma kun kasa kunne ga umarnina kurum! Da sai albarka ta yi ta kwararowa dominku Kamar ƙoramar da ba ta taɓa ƙafewa ba! Da kuma nasara ta samu a gare ku kamar raƙuman ruwa Da suke bugowa zuwa gāɓa.
19
Zuriyarku za su yi yawa kamar tsabar yashi, Zan kuma tabbatar, cewa ba za a hallaka su ba.”
20
Ku fita daga Babila, ku tafi a sake! Ku yi sowar albishir da farin ciki, ku sa a sani a ko'ina, “Ubangiji ya fanshi bawansa Isra'ila!”
21
Lokacin da Ubangiji ya bi da mutanensa ta cikin busasshiyar hamada, mai zafi, Ba su sha wahalar ƙishi ba. Ya sa ruwa ya gudano daga cikin dutse dominsu, Ya tsage dutse, ruwa ya kwararo.
22
Ubangiji ya ce, “Ba mafaka domin masu zunubi.”
← Chapter 47
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 49 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64
65
66