bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Isaiah 34
Isaiah 34
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 33
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 35 →
1
Ku zo, ku jama'ar dukan al'ummai! Ku tattaru ku kasa kunne. Bari dukan duniya, da kowane mai zama cikinta, ya zo nan ya kasa kunne.
2
Ubangiji yana fushi da al'ummai duka, da kuma dukan sojojinsu. Ya zartar musu da hukuncin hallaka.
3
Ba za a binne gawawwakinsu ba, amma za a bar su can, su ruɓe, su yi ɗoyi, duwatsu kuma za su yi ja wur da jini.
4
Za a murtsuke rana, da wata, da taurari su zama ƙura. Sararin sama zai shuɗe kamar yadda ake naɗe littafi, taurari kuma su faɗo kamar yadda ganyaye suke karkaɗewa daga itacen inabi ko na ɓaure.
5
Ubangiji ya shirya takobinsa a can Sama, yanzu kuwa zai buga Edom, wato mutanen can da ya zartar musu da hukuncin hallaka.
6
Jininsu da kitsensu za su rufe takobinsa, kamar jini da kitsen raguna, da na awaki, da aka miƙa hadaya. Ubangiji zai yi wannan hadaya a birnin Bozara, zai sa wannan ya zama babban kisa a ƙasar Edom.
7
Mutane za su fāɗi kamar bijiman jeji da 'yan bijimai, ƙasar za ta yi ja wur da jini, kitse kuma zai rufe ta.
8
Wannan shi ne lokacin da Ubangiji zai kuɓutar da Sihiyona, ya kuma ɗauki fansa a kan abokan gābanta.
9
Kogunan Edom za su zama kalo, wato kwalta, ƙasar za ta zama kibritu, wato farar wuta. Dukan ƙasar za ta ƙone kamar kalo.
10
Za ta yi ta ci dare da rana, hayaƙi zai yi ta tashi sama har abada. Ƙasar za ta zama marar amfani shekara da shekaru, ba wanda zai iya ƙara bi ta cikinta.
11
Mujiyoyi da hankaki su ne za su gāji ƙasar. Ubangiji zai maishe ta marar amfani, kamar yadda take tun kafin halitta.
12
Ba sarkin da zai yi mulkin ƙasar, dukan shugabanni kuma za su ƙare.
13
Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su tsiro su yi girma a cikin dukan fādodi da garuruwa masu garuka, diloli da mujiyoyi za su zauna a cikinsu.
14
Namomin jeji za su yi ta kaiwa da komowa a can suna kiran juna. Mugun naman jeji zai je can ya nemi wurin hutawa.
15
Mujiyoyi za su yi sheƙarsu a can, su nasa ƙwayaye, su ƙyanƙyashe 'ya'yansu, su kuma lura da su a can. Ungulai za su tattaru a can a kai a kai.
16
Bincika cikin Littafin Ubangiji ka karanta abin da yake faɗa. Ba ko ɗaya cikin halittattun nan da zai ɓata ba, ba kuwa wanda zai rasa ɗan'uwansa. Ubangiji ne ya umarta ya zama haka, shi kansa zai kawo su tare.
17
Ubangiji ne zai rarraba musu ƙasar, ya kuma ba ko wannensu nasa rabo. Za su zauna a ƙasar shekara da shekaru, za ta kuwa zama tasu har abada.
← Chapter 33
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 35 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64
65
66