bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Isaiah 7
Isaiah 7
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 6
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 8 →
1
Sa'ad da sarki Ahaz, ɗan Yotam, wato jikan Azariya yake mulkin Yahuza, sai yaƙi ya ɓarke. Rezin, Sarkin Suriya, da Feka ɗan Remaliya, Sarkin Isra'ila, suka fāɗa wa Urushalima da yaƙi, amma ba su iya cinta ba.
2
Labari ya kai gun Sarkin Yahuza, cewa sojojin Suriya sun shiga ƙasar Isra'ila. Sai shi da dukan jama'arsa suka firgita ƙwarai, suna ta kaɗuwa kamar itatuwan da iska take kaɗawa.
3
Ubangiji ya ce wa Ishaya, “Ka ɗauki ɗanka Sheyar-yashub ka je ka sami sarki Ahaz. Za ka same shi a hanya inda masu wankin tufafi suke aiki, a wajen ƙarshen wuriyar da yake kawo ruwa daga kududdufin da yake sama da ita.
4
Faɗa masa ya zauna da shiri, ya natsu, kada ya ji tsoro ko ya damu. Fushin sarki Rezin da Suriyawansa da na sarki Feka ba wani abu mai hatsari ba ne, bai fi hayaƙin 'yan ƙirare biyu da suke cin wuta ba.
5
Suriya tare da Isra'ila da sarkinta sun ƙulla maƙarƙashiya.
6
Nufinsu su kai wa ƙasar Yahuza yaƙi, su tsoratar da jama'a, don su haɗa kai da su, sa'an nan su naɗa ɗan Tabeyel.
7
“Amma ni Ubangiji na hurta, faufau wannan ba zai faru ba.
8
Don me? Saboda Dimashƙu ita ce ƙarfin Suriya, sarki Rezin kuwa shi ne ƙarfin Dimashƙu. Isra'ila kuwa a shekara sittin da biyar masu zuwa za ta karkasu, har ba za ta iya rayuwa ta zama al'umma ba.
9
Samariya ita ce ƙarfin Isra'ila, sarki Feka kuma shi ne ƙarfin Samariya. “Idan bangaskiyarku ba ta da ƙarfi, to, ba za ku dawwama ba.”
10
Ubangiji ya aika wa Ahaz da wani jawabi, ya ce,
11
“Ka roƙi Ubangiji Allahnka ya ba ka alama. Yana yiwuwa daga can zurfin lahira ne, ko kuma daga can cikin sama ne.”
12
Ahaz ya amsa, ya ce, “Ba zan nemi wata alama ba. Ba zan jarraba Ubangiji ba.”
13
Ga amsar da Ishaya ya ba Ahaz, “Kasa kunne yanzu, kai zuriyar sarki Dawuda. Ba abin kirki kuke yi ba, da kuka ƙure haƙurin jama'a, haƙurin Allah kuma kuke so ku ƙure?
14
Yanzu fa, Ubangiji kansa zai ba ku alama. Wata budurwa wadda take da ciki, za ta haifi ɗa, za a raɗa masa suna Immanuwel.
15
In ya yi girma har ya isa yanke shawara don kansa, madara da zuma ne abincinsa.
16
Kafin lokacin ya yi, ƙasashen sarakunan nan biyu waɗanda suka firgita ku za su zama kango.
17
“Ubangiji zai aukar maka da kwanakin wahala, kai da jama'arka, da dukan iyalin gidan sarauta, waɗanda suka fi muni tun lokacin da aka raba mulkin Isra'ila daga na Yahuza. Zai kawo Sarkin Assuriya!
18
“A lokacin nan, Ubangiji zai yi feɗuwa ya kirawo Masarawa su zo kamar ƙudaje daga manisantan mazaunan Kogin Nilu, ya kuma kirawo Assuriyawa su zo daga ƙasarsu kamar ƙudajen zuma.
19
Za su zo jingim su mamaye kwazazzabai da kogwanni cikin duwatsu, za su rufe kowane fili mai ƙayayuwa da kowace makiyaya.
20
“A lokacin nan, Ubangiji zai yi ijara da wanzami daga wancan hayi na Yufiretis, wato Sarkin Assuriya! Zai aske gyammanku, da gashin kawunanku, da na jikunanku.
21
“A lokacin nan, ko da karsana ɗaya da awaki biyu kaɗai manomi yake da su,
22
za su ba da isasshiyar madarar da za ta biya dukan bukatarsa. Hakika dukan waɗanda suka ragu a ƙasar za su sami yawan albarka su ƙoshi.
23
“A lokacin nan, waɗannan kyawawan gonakin inabi waɗanda suke da kurangar inabi dubu, kuɗin kowace gonar inabi azurfa dubu guda ne, gonakin za su cika da ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya.
24
Ba wanda yake da ƙarfin hali da zai iya tafiya can, sai ko wanda yake da kwari da baka. Hakika ƙasar duka za ta cika da sarƙaƙƙiya da ƙayayuwa.
25
Dukan tuddai inda dā akan shuka amfanin gona, za su cika da ƙayayuwa, har da ba mai iya zuwa wurin. Zai zama wurin kiwon shanu da tumaki.”
← Chapter 6
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 8 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64
65
66