bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Isaiah 41
Isaiah 41
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 40
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 42 →
1
Allah ya ce, “Ku yi shiru ku kasa kunne gare ni, ku manisantan ƙasashe! Ku yi shiri ku gabatar da ƙararku a ɗakin shari'a. Za ku sami zarafi ku yi magana. Bari mu taru mu ga wanda yake da gaskiya.
2
“Wane ne wannan da ya kawo mai yin nasara daga gabas, Ya kuma sa ya ci nasara a dukan inda ya tafi? Wa ya ba shi nasara a kan sarakuna da al'ummai? Takobinsa ya sassare su sun zama kamar ƙura! Kibansa sun warwatsar da su kamar ƙaiƙayi a gaban iska!
3
Yana biye da kora, yana kuma tafiya lafiya, Da sauri ƙwarai, da ƙyar yake taɓa ƙasa!
4
Wane ne ya sa wannan ya faru? Wane ne ya ƙudurta labarun tarihi? Ni Ubangiji, ina can tun da farko, Ni kuma Ubangiji Allah, Zan kasance a can har ƙarshe.
5
“Mutanen manisantan ƙasashe suka ga abin da na yi, Suka tsorata, suka yi rawar jiki saboda tsoro. Saboda haka duka suka tattaru wuri guda.
6
Masu aikin hannu suka taimaka suka ƙarfafa juna.
7
Masassaƙi yakan ce wa maƙerin zinariya, ‘A gaishe ka!’ Wanda yake gyara gumaka ya yi sumul Yana ƙarfafa wanda yake harhaɗa su. Wani yakan ce, ‘Haɗin ya yi kyau,’ Sukan kuma manne gumakan da ƙusoshi.
8
“Amma kai, Isra'ila bawana, Kai ne jama'ar da na zaɓa, Zuriyar Ibrahim, abokina,
9
Na kawo ka daga maƙurar duniya, Na kira ka daga kusurwoyi mafi nisa. Na ce maka, ‘Kai ne bawana.’ Ban ƙi ka ba, amma maimakon haka na zaɓe ka.
10
Kada ka ji tsoro, ina tare da kai, Ni ne Allahnka, kada ka bar kome ya firgita ka. Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka, Zan kiyaye ka, in cece ka.
11
“Su waɗanda suke fushi da ku, ku jama'ata, Za a ƙasƙantar da su su ji kunya. Waɗanda suke faɗa da ku kuwa za su mutu.
12
Za ku neme su, amma ba za ku same su ba, Wato waɗanda suke gāba da ku. Waɗanda suka kama yaƙi da ku, Za su shuɗe daga duniya.
13
Ni ne Ubangiji Allahnku, Na ƙarfafa ku, na kuwa faɗa muku, ‘Kada ku ji tsoro, ni zan taimake ku.’ ”
14
Ubangiji ya ce, “Isra'ila, ku kima ne marasa ƙarfi kuma, Kada ku ji tsoro, zan taimake ku. Ni Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ni ne mai fansarku.
15
Zan sa ku zama kamar abin sussuka, Wanda yake sabo, mai kaushi, mai tsini. Za ku sussuke duwatsu ku lalatar da su, Za a marmashe tuddai kamar ƙura.
16
Za ku watsa su sama cikin iska, Iska za ta hure su, ta tafi da su, Hadiri kuma zai warwatsar da su. Amma za ku yi murna, gama ni ne Allahnku, Za ku yabe ni, Allah Mai Tsarki na Isra'ila.
17
“Sa'ad da jama'ata ta bukaci ruwa, Sa'ad da maƙogwaronsu ya bushe da ƙishi, Sa'an nan ni Ubangiji, zan amsa addu'arsu, Ni Allah na Isra'ila, ba zan taɓa yashe su ba.
18
Zan sa kogunan ruwa su yi gudu daga ƙeƙasassun tuddai, Maɓuɓɓugan ruwa su yi gudu a kwaruruka. Zan sa hamada ta zama kududdufan ruwa, Busasshiyar ƙasa kuma ta zama maɓuɓɓugan ruwa.
19
Zan sa itatuwan al'ul su tsiro a hamada, Da itacen ƙirya, da itacen ci-zaki, da zaitun. Ƙeƙasasshiyar ƙasa za ta zama kurmi, Jejin itatuwan fir.
20
Mutane za su ga wannan, su sani, Ni Ubangiji, na yi shi. Za su fahimta, Allah Mai Tsarki na Isra'ila ya sa abin ya faru.”
21
Ubangiji, Sarki na Isra'ila, ya faɗi wannan, “Ku allolin al'ummai ku gabatar da matsalarku. Ku kawo dukan gardandamin da kuke da su!
22
Ku zo nan ku faɗi abin da zai faru nan gaba, Ku bayyana wa ɗakin shari'a abubuwan da suka riga sun faru, Ku faɗa mana yadda zai zama duka, Domin lokacin da ya faru mu mu sani.
23
Ku faɗa mana abin da gaba ta ƙunsa. Sa'an nan za mu sani, ku alloli ne! Ku aikata wani abu mai kyau, ko ku kawo wani bala'i, Ku cika mu da jin tsoro da fargaba!
24
Ku da dukan abin da kuke yi ba kome ba ne, Waɗanda suke yi muku sujada kuwa, Abin ƙyama ne su!
25
“Na zaɓi mutum wanda yake zaune a gabas, Zan kawo shi don ya kawo hari daga arewa. Zai tattake masu mulki su zama kamar lāka, Kamar yadda magini yake tattake yumɓu.
26
Wane ne a cikinku ya faɗa mana tun da wuri, Ko ya yi annabci, cewa wannan zai faru, Har da za mu ce kun yi daidai? Ba ko ɗayanku da ya ce tak a kan wannan, Ba kuwa wanda ya ji kuna faɗar wani abu!
27
Ni Ubangiji, ni ne na farko da na faɗa wa Sihiyona albishir, Na aiki manzo zuwa Urushalima don ya ce, ‘Jama'arki suna zuwa! Suna zuwa gida.’
28
Sa'ad da na duba alloli, Ba wanda yake da abin da zai faɗa, Ko ɗaya, ba wanda ya iya amsa tambayar da na yi.
29
Dukan waɗannan alloli ba su da amfani, Ba su iya kome ba, ko kaɗan, Gumakansu ba su da ƙarfi, ba su kuma da iko!”
← Chapter 40
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 42 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64
65
66