bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Isaiah 31
Isaiah 31
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 30
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 32 →
1
Waɗanda suka tafi Masar neman taimako, sun shiga uku! Suna dogara ga ƙarfin tulin dawakan Masar na yaƙi, da karusansu, da sojojinsu. Amma ba su dogara ga Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila ba, ba su ko roƙe shi taimako ba.
2
Ya san abin da yake yi! Zai aika da bala'i. Zai ci gaba da niyyarsa ta hukunta wa mugaye duk da masu kiyaye su.
3
Masarawa su ba Allah ba ne, mutane ne kurum! Dawakansu ba su wuce ikon ɗan adam ba! Sa'ad da Ubangiji zai matsa, ƙaƙƙarfar al'umma za ta marmashe, al'ummar da aka yi wa taimako kuma za ta fāɗi. Dukansu za su hallaka.
4
Ubangiji ya ce mini, “Kamar dai makiyaya ba za su iya tsoratar da zakin da ya kashe dabba ba, kome irin tsawa da ihun da suka yi, haka ni ma, ba abin da zai iya hana ni, ni Ubangiji Mai Runduna, in kiyaye Dutsen Sihiyona.
5
Kamar yadda tsuntsu yake shawagi a kan sheƙarsa don ya kiyaye 'ya'yansa, haka ni, Ubangiji Mai Runduna, zan kiyaye Urushalima in kāre ta kuma.”
6
Allah ya ce, “Jama'ar Isra'ila, kun yi mini zunubi, kuna kuwa yin gāba da ni. Amma yanzu ku komo wurina!
7
Lokaci zai yi da dukanku za ku watsar da gumakan da kuka yi na azurfa da na zinariya.
8
Assuriya za ta hallaka cikin yaƙi, amma ba ta wurin ikon mutum ba. Assuriyawa za su gudu daga bakin dāga, za a mai da majiya ƙarfinsu bayi.
9
Sarkinsu zai tsere saboda razana, shugabannin sojojinsu kuwa za su firgita, har su watsar da tutocinsu na yaƙi.” Ubangiji ne ya faɗa, Ubangiji da ake yi wa sujada a Urushalima, wanda kuma wutarsa tana ci a can domin hadayu.
← Chapter 30
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 32 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64
65
66