bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Ezekiel 17
Ezekiel 17
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 16
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 18 →
1
Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,
2
“Ɗan mutum, ka faɗa wa mutanen Isra'ila ka-cici-ka-cici, da kuma misali.
3
Ka ce, Ubangiji Allah ya ce, ‘Wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai, da dogayen gasusuwan fikafikai da gasusuwa da yawa masu launi iri iri, ta zo Lebanon ta ciri kan itacen al'ul.
4
Ta karya kan tohonsa mafi tsawo, ta kai shi a ƙasar ciniki, ta dasa shi a birnin 'yan kasuwa.
5
Sai kuma ta ɗauki irin na ƙasar, ta dasa shi a wuri mai dausayi kusa da ruwa mai yawa. Ta dasa shi kamar itacen wardi.
6
Ya yi toho, ya zama kuranga mai yaɗuwa. Rassanta suka tanƙwasa wajenta. Saiwoyinta suka kama ƙasa sosai. Haka ta zama kuranga, ta yi rassa da ganyaye.
7
“ ‘Akwai kuma wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai da gashi mai yawa. Sai wannan kuranga ta tanƙwasa saiwoyinta zuwa wajenta, ta kuma miƙe rassanta zuwa wajenta tun daga inda aka dasa ta, don gaggafar ta yi mata banruwa.
8
An dasa ta a wuri mai dausayi inda akwai ruwa da yawa don ta yi ganyaye, ta kuma ba da 'ya'ya, ta zama kurangar inabi ta ƙwarai.’
9
Ka ce, Ubangiji Allah ya ce, ‘Ko wannan kurangar inabi za ta ci gaba? Ashe, gaggafa ta farko ba za ta tumɓuke saiwoyinta, ta sassare rassanta, don ganyayenta da suke tohuwa su bushe ba? Ba sai da hannu mai ƙarfi, ko kuwa da yawan mutane za a tumɓuke ta daga saiwoyinta ba.
10
Idan aka sāke dasa ta kuma za ta yi amfani? Ba za ta bushe sarai sa'ad da iskar gabas ta hura ba? Lalle za ta bushe tun daga inda aka dasa ta ta yi girma.”’
11
Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,
12
“Ka tambayi mutanen Isra'ila, 'yan tawayen nan cewa, ‘Ba ku san ma'anar waɗannan abubuwa ba?’ Ka faɗa musu, cewa Sarkin Babila ya zo Urushalima, ya tafi da sarkinta da shugabanninta zuwa Babila.
13
Sai ya dauƙi wani daga zuriyar sarauta, ya yi alkawari da shi, ya kuma rantsar da shi. Ya kwashe mutanen ƙasa masu maƙami,
14
don sarautar ƙasar ta raunana, ta kāsa ɗaga kanta, amma ta tsaya dai ta wurin cika alkawarinsa.
15
Amma Sarkin Yahuza ya tayar masa, da ya aiki wakilai zuwa Masar don a ba shi dawakai da sojoji masu yawa. To, zai yi nasara? Wanda ya yi irin wannan abu zai tsira? Zai iya ta da alkawari sa'an nan ya tsere?
16
“Ni Ubangiji Allah, na ce, hakika wannan sarki zai mutu a Babila, domin bai cika rantsuwarsa da alkawarin da ya yi wa Sarkin Babila, wanda ya naɗa shi ba.
17
Fir'auna da yawan sojojinsa masu ƙarfi, ba za su taimake shi da yaƙin ba, sa'ad da Babilawa suka gina mahaurai da kagarai don su kashe mutane da yawa.
18
Bai kuwa cika rantsuwarsa da alkawarinsa ba. Ya ƙulla alkawari, amma ga shi, ya aikata dukan waɗannan abubuwa, ba zai kuɓuta ba.
19
“Domin haka ni Ubangiji Allah, na ce, hakika zan nemi hakkin rantsuwar da ya yi mini, da alkawarin da ya yi mini, waɗanda bai cika ba.
20
Zan kafa masa tarko in kama shi, sa'an nan in kai shi Babila inda zan yi masa shari'a saboda ya tayar mini.
21
Dukan sojojinsa zaɓaɓɓu za a kashe su da takobi, za a watsar da waɗanda suka ragu ko'ina. Za ku sani ni Ubangiji ne na faɗa.”
22
Ga abin da Ubangiji Allah ya ce, “Ni kaina zan cire toho a kan itacen al'ul mai tsawo. Daga cikin sababbin rassansa zan karya lingaɓu, In dasa shi a tsauni mai tsayi.
23
A ƙwanƙolin tsaunin Isra'ila zan dasa shi Don ya fito da rassa, ya ba da 'ya'ya, Ya zama itacen al'ul na gaske. Tsuntsaye iri iri za su zauna a ƙarƙashinsa, Za su yi sheƙuna a cikin inuwar rassansa.
24
Dukan itatuwan jeji za su sani, Ni Ubangiji nakan sa manyan itatuwa su zama ƙanana, In sa ƙanana kuma su zama manya, In sa ɗanyen itace ya bushe, In sa busasshen itace kuma ya zama ɗanye, Ni Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata.”
← Chapter 16
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 18 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48