bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Ezekiel 32
Ezekiel 32
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 31
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 33 →
1
A kan rana ta fari, ga watan goma sha biyu, a shekara ta goma sha biyu, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
2
“Ɗan mutum, ka yi makoki a kan Fir'auna, Sarkin Masar, ka ce, ‘Ka aza kanka kamar zaki a cikin al'ummai, Amma kai kada ne a cikin ruwa. Ka ɓullo cikin kogunanka, Ka gurɓata ruwa da ƙafafunka, Ka ƙazantar da kogunansu.’
3
Ubangiji Allah ya ce, ‘Zan jefa taruna a kanka, a babban taron mutane, Zan jawo ka cikin taruna.
4
Zan jefar da kai a tudu, A fili zan jefa ka. Zan sa tsuntsayen sararin sama su ɗira a kanka, Zan ƙosar da namomin jeji na dukan duniya da namanka.
5
Zan watsa namanka a kan duwatsu, In cika kwaruruka da gawarka.
6
Zan watsar da jininka a ƙasa da tuddai, Magudanan ruwa za su cika da jininka.
7
Sa'ad da na shafe ka, zan rufe sammai, In sa taurarinsu su duhunta, Zan sa girgije ya rufe rana, Wata kuma ba zai haskaka ba.
8
Dukan haskokin sama zan sa su zama duhu a gare ka, In sa ƙasarka ta duhunta, ni Ubangiji Allah na faɗa.’
9
“Zukatan al'ummai da yawa za su ɓaci, sa'ad da na baza labarin halakarka a ƙasashen da ba ka sani ba.
10
Al'ummai da yawa za su gigice saboda abin da zai same ka, sarakunansu kuma za su yi rawar jiki saboda kai sa'ad da na kaɗa takobi a gabansu. A ranar faɗuwarka za su yi rawar jiki a kowane lokaci, kowa saboda ransa.”
11
Ubangiji Allah ya ce, “Takobin Sarkin Babila zai auko maka.
12
Zan sa ƙarfafan mutane masu bantsoro daga cikin al'ummai su kashe jama'arka da takuba. Za su wofinta girmankan Masar, Su kuma hallaka jama'arta.
13
Zan hallaka dukan dabbobinta da suke bakin ruwa, Ba ƙafar mutum ko ta dabba da za ta ƙara gurɓata ruwa.
14
Zan sa ruwansu ya yi garau, In sa kogunansu su malala kamar mai, Ni Ubangiji Allah na faɗa.
15
Sa'ad da na mai da ƙasar Masar kufai, In raba ƙasar da abin da take cike da shi, Sa'ad da na bugi dukan waɗanda suke cikinta, Daga nan za su sani ni ne Ubangiji.
16
Wannan ita ce waƙar makokin. 'Yan matan al'ummai za su raira wa Masar da jama'arta duka, ni Ubangiji Allah na faɗa.”
17
A rana ta goma sha biyar ga wata na fari, a shekara ta goma sha biyu, Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
18
“Ɗan mutum, ka yi kuka saboda jama'ar Masar. Ka tura su tare da sauran al'umma zuwa lahira wurin waɗanda suka gangara zuwa cikin kabari.
19
Ka ce, ‘Su wa kika fi kyau? Ki gangara, ki kwanta tare da marasa imani.’
20
“An zare takobi don a kashe jama'ar Masar. Za su fāɗi a tsakiyar waɗanda aka kashe da takobi.
21
Manyan jarumawa daga lahira za su yi magana a kansu da mataimakansu, su ce, ‘Marasa imani waɗanda aka kashe da takobi, sun gangaro, ga su nan kwance shiru!’
22
“Assuriya tana can da dukan taron jama'arta. Kaburburansu suna kewaye da ita. An kashe dukansu da takobi.
23
An binne su a can ƙurewar lahira. Taron jama'arta suna kewaye da kabarinta. An kashe dukansu da takobi. Su ne suka haddasa tsoro a cikin ƙasar.
24
“Elam tana can da dukan jama'arta kewaye da kabarinta. An kashe dukansu da takobi. Sun gangara da rashin imaninsu zuwa lahira. Su ne suka haddasa tsoro a duniya. Sun sha kunyarsu tare da waɗanda suka gangara zuwa kabari.
25
An shirya mata gado tare da matattu. Kaburburan dukan sojojinta suna kewaye. Dukansu marasa imani ne, waɗanda aka kashe da takobi, amma a dā sun yaɗa tsoro a duniya. Yanzu kuwa suna shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa kabari. An tara su tare da waɗanda aka kashe.
26
“Meshek da Tubal suna can da dukan sojojinsu. Kaburburan sojojinsu suna kewaye. Dukansu marasa imani ne, waɗanda aka kashe da takobi, gama sun yaɗa tsoro a duniya.
27
Ba su kwanta kusa da manyan jarumawan da aka kashe ba, waɗanda suka tafi lahira da makamansu, aka yi musu matasan kai da takubansu, aka rufe ƙasusuwansu da garkuwoyinsu, gama manyan jarumawan nan sun baza tsoro a duniya.
28
Amma za a karya ku, ku kwanta tare da marasa imani, tare da waɗanda aka kashe da takobi.
29
“Edom kuma tana can tare da sarakunanta da dukan shugabanninta masu iko, Suna kwance tare da waɗanda aka kashe da takobi, marasa imani, masu gangarawa zuwa cikin kabari.
30
“Dukan shugabannin arewa suna can, da dukan Sidoniyawa. Da kunya, suna gangarawa tare da waɗanda aka kashe, ko da yake a dā sun haddasa tsoro saboda ikonsu. Yanzu suna kwance tare da marasa imani waɗanda aka kashe da takobi. Suna shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa cikin kabari.
31
“Sa'ad da Fir'auna zai gan su, zai ta'azantu a kan rundunarsa da aka kashe da takobi. Lalle Fir'auna da dukan rundunarsa za su ta'azantu. Ni Ubangiji Allah na faɗa.
32
“Ko da yake na sa Fir'auna ya haddasa tsoro a duniya, duk da haka zan sa a kashe shi tare da rundunarsa. Za su kwanta tare da marasa imani waɗanda aka kashe da takobi. Ni Ubangiji Allah na faɗa.”
← Chapter 31
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 33 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48