bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Ezekiel 4
Ezekiel 4
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 3
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 5 →
1
“Ya kai ɗan mutum, sai ka ɗauki tubali, ka ajiye a gabanka, sa'an nan ka zāna birni a kansa, wato Urushalima.
2
Sa'an nan ka gina mata kagara, da garu da ɗan tudu. Ka kuma kafa mata sansani ka kewaye ta da dundurusai.
3
Ka ɗauki kwano, ka shirya shi kamar garun ƙarfe tsakaninka da birnin, sa'an nan ka zuba ido. Birnin zai zama kamar an kewaye shi da yaƙi, kai kuwa ka kewaye shi da yaƙi. Wannan kuma zai zama alama ga Isra'ilawa.
4
“Sai kuma ka kwanta a hagunka, ni kuwa zan ɗora maka muguntar Isra'ilawa. Za ka ɗauki muguntarsu bisa ga yawan kwanakin da za ka kwanta a hagunka.
5
Gama na ɗora maka kwanaki bisa ga shekarun muguntarsu, wato kwana ɗari uku da tasa'in da za ka kwanta. Ta haka za ka ɗauki alhakin muguntar mutanen Isra'ila.
6
Sa'ad da ka cika waɗannan kwanaki, sai ka sāke kwantawa, kwanciya ta biyu, a damanka kwana arba'in don ka ɗauki alhakin muguntar mutanen Yahuza. Kwana ɗaya a bakin shekara guda.
7
“Za ka fuskanci Urushalima wadda aka kewaye ta da yaƙi da hannunka a zāge, sa'an nan ka yi annabci a kanta.
8
Ga shi, zan ɗaure ka da igiyoyi don kada ka juya har ka gama misalin adadin kwanakin da za a kewaye Urushalima da yaƙi.
9
“Ka kuma ɗauki alkama, da sha'ir, da wake, da waken soya, da gero, da acca, ka haɗa su a kasko ɗaya, ka yi abinci da su. Shi ne za ka ci a kwanakin na ɗari uku da tasa'in da za ka kwanta.
10
Za a auna maka abincin da za ka ci, kamar nauyin shekel ashirin ne a yini. Za ka ci shi a ƙayyadadden lokaci kowace rana.
11
Za a kuma auna maka ruwan da za ka sha, misalin kwalaba biyu ga yini. Za ka sha ruwan a ƙayyadadden lokaci kowace rana.
12
Za ka yi waina kamar ta sha'ir, ka ci. Za ka toya ta da najasa a idon jama'a.”
13
Ubangiji ya ce, “Haka jama'ar Isra'ila za su ci ƙazantaccen abincinsu a cikin sauran al'umma inda za a kai su bautar talala.”
14
Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah, ban taɓa ƙazantar da kaina ba. Tun daga ƙuruciyata har zuwa yau, ban taɓa cin mushe ba, ko abin da namomin jeji suka kashe. Ƙazantaccen nama bai taɓa shiga bakina ba.”
15
Sa'an nan ya ce mini, “To, zan bar ka ka mori taroson shanu maimakon najasa, don ka dafa abincinka.”
16
Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ga shi, zan datse abinci a Urushalima. Za su auna abincin da za su ci da tsoro, su kuma auna ruwan da za su sha da damuwa.
17
Haka abinci da ruwa za su kāsa, za su kuwa dubi juna da damuwa. Za su lalace saboda zunubansu.”
← Chapter 3
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 5 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48