bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Ezekiel 46
Ezekiel 46
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 45
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 47 →
1
“Ni Ubangiji Allah na ce za a rufe ƙofar fili ta can ciki wadda take fuskantar gabas dukan ranaku shida na aiki, amma za a buɗe ta a ranar Asabar da a amaryar wata.
2
Sarki zai shiga ta ƙofar shirayi daga waje, sa'an nan ya tsaya kusa da ginshiƙin ƙofar. Sai firistoci su miƙa hadayarsa ta ƙonawa, da hadayunsa na salama, shi kuwa ya yi sujada s bakin ƙofar, sa'an nan ya fita, amma ba za a rufe ƙofar ba sai da maraice.
3
Jama'ar ƙasar za su yi wa Ubangiji sujada a bakin wannan ƙofa a ranakun Asabar da a amaryar wata.
4
Hadaya ta ƙonawa da sarki zai miƙa wa Ubangiji a ranar Asabar 'yan raguna shida ne da rago ɗaya marasa lahani.
5
Gārin hadaya da za a yi tare da rago wajen garwa guda ne. Wanda za a yi tare da 'yan raguna kuwa zai zama gwargwadon ƙarfinsa. Zai ba da mai wajen kwalaba shida domin kowace garwa ta gari.
6
A amaryar wata kuwa zai miƙa bijimi, da 'yan raguna shida, da rago, dukansu marasa lahani.
7
Gārin hadayar da za a yi tare da bijimin wajen garwa guda ne, haka kuma gari na wadda za a yi tare da ragon, da gari na wadda za a yi tare da 'yan raguna kuma, zai zama gwargwadon ƙarfinsa. Zai ba da man zaitun wajen kwalaba shida domin kowace garwa ta garin.
8
Sa'ad da sarki zai shiga, sai ya shiga ta ƙofar shirayin, ya kuma fita ta nan.
9
“Sa'ad da jama'ar ƙasar sun zo yi wa Ubangiji sujada a lokatan ƙayyadaddun idodi, wanda ya shiga ta ƙofar arewa, sai ya fita ta ƙofar kudu. Wanda kuma ya shiga ta ƙofar kudu, sai ya fita ta ƙofar arewa. Kada kowa ya fita ta ƙofar da ya shiga, amma sai kowa ya fita ta akasin ƙofar da ya shiga.
10
Sa'ad da suka shiga, sai sarki ya shiga tare da su, sa'ad da suka fita kuma, sai ya fita.
11
A lokacin idodi da ƙayyadaddun lokatai, gārin hadayar da za a yi tare da bijimi wajen garwa guda ne, haka kuma na wadda za a yi tare da ragon, na wadda za a yi tare da 'yan ragunan kuwa, sai mutum ya kawo gwargwadon ƙarfinsa. A kuma kawo wajen kwalaba shida na man zaitun domin kowace garwa ta gari.
12
“Sa'ad da sarki ya kawo hadayar ƙonawa ko hadayar salama ta yardar rai ga Ubangiji, sai a buɗe masa ƙofar da take fuskantar gabas. Zai kuwa miƙa hadayarsa ta ƙonawa ko ta salama kamar yadda yakan yi a ranar Asabar. Bayan da ya fita, sai a rufe ƙofa.
13
“Kowace safiya za a yi hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji da ɗan rago bana ɗaya marar lahani.
14
Tare da hadaya ta ƙonawa, za a ba da wajen ɗaya bisa shida na garwar gari, da kwalaba biyu na man zaitun don cuɗa gari, domin a yi hadaya ga Ubangiji. Wannan ita ce ka'idar hadaya ta ƙonawa ta yau da kullum.
15
Za a ba da ɗan rago, da gari, da mai, kowace safiya domin yin hadaya ta ƙonawa.
16
“Ni Ubangiji Allah na ce, idan sarki ya yi wa wani daga cikin 'ya'yansa kyauta daga cikin gādonsa, sai kyautar ta zama ta 'ya'yansa, dukiyarsu ce ta gādo.
17
Amma idan sarki ya yi wa wani daga cikin barorinsa kyauta daga cikin gādonsa, kyautar za ta zama tasa har shekarar 'yantarwa, sa'an nan kyautar za ta koma a hannun sarki. 'Ya'yansa maza ne kaɗai za su riƙe kyauta daga cikin gādonsa din din din.
18
Kada sarki ya ƙwace rabon gādon jama'a, ya hana musu. Sai ya ba 'ya'yansa maza rabon gādo daga cikin abin da yake nasa, amma kada ya ƙwace wa jama'ata abin da suka mallaka har su warwatse.”
19
Sai mutumin ya bi da ni ta hanyar da take gefen ƙofa mai fuskantar arewa, wajen jerin tsarkakakkun ɗakuna na firistoci, waɗanda suke fuskantar arewa. Na kuma ga wani wuri daga can ƙurewar yamma.
20
Sai ya ce mini, “Wannan shi ne wurin da firistoci za su dafa hadaya domin laifi, da hadaya domin zunubi, a nan ne kuma za su toya hadaya ta gāri, domin kada su kai su a filin waje, su sa wa mutane tsarki.”
21
Ya kuma kai ni a farfajiyar waje, ya bi da ni zuwa kusurwa huɗu na farfajiya. Akwai ɗan fili a kowace kusurwa.
22
Girman kowane ɗan fili tsawonsa kamu arba'in ne, faɗin kuma kamu talatin.
23
A cikin kowane ɗan fili na kusurwa huɗu ɗin akwai jerin duwatsu. Aka gina murhu ƙarƙashin jerin duwatsun.
24
Sa'an nan ya ce mini, “Waɗannan su ne ɗakunan dahuwa inda masu hidima a Haikali za su dafa hadayun da jama'a suka kawo.”
← Chapter 45
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 47 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48