bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Ezekiel 37
Ezekiel 37
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 36
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 38 →
1
Ikon Ubangiji kuwa ya sauko a kaina, Ruhunsa kuma ya fito da ni ya ajiye ni a tsakiyar kwari wanda yake cike da ƙasusuwa.
2
Sai ya zagaya da ni cikinsu, ga su kuwa, suna da yawa a cikin kwarin, busassu ragau.
3
Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan ƙasusuwa kuwa za su rayu?” Ni kuwa na amsa na ce, “Ya Ubangiji Allah, sani na gare ka.”
4
Sai ya ce mini, “Ka yi annabci a kan ƙasusuwan nan ka faɗa musu su saurari maganata.
5
Gama ni Ubangiji Allah zan hura musu numfashi, za su kuwa rayu.
6
Zan sa musu jijiyoyi da tsoka, in rufe da fata, in kuma hura musu numfashi, sa'an nan za su rayu, su sani ni ne Ubangiji.”
7
Sai na yi annabci kamar yadda ya umarce ni. Da na yi annabcin sai aka ji motsi da girgiza. Sai ƙasusuwan suka harhaɗu da juna, ƙashi ya haɗu da ƙashi a mahaɗinsu.
8
Da na duba, sai ga jijiyoyi a kansu, nama kuma ya baibaye su, sa'an nan fata ta rufe su, amma ba numfashi a cikinsu.
9
Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, ka yi annabci a kan iska, ka ce mata, ni Ubangiji Allah na ce ta zo daga kusurwa huɗu, ta hura a kan waɗannan matattu domin su rayu.”
10
Na kuwa yi annabci kamar yadda aka umarce ni, sai numfashi ya shiga cikinsu, suka rayu, suka tashi, suka tsaya da ƙafafunsu. Sun zama babbar runduna ƙwarai.
11
Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum waɗannan ƙasusuwa su ne mutanen Isra'ila duka. Ga shi, suna cewa, ‘Ƙasusuwa sun bushe, zuciyarmu kuwa ta karai, an share mu ƙaƙaf.’
12
“Domin haka ka yi annabci ka ce musu, ni Ubangiji Allah na ce zan buɗe kaburburansu, in tashe su daga cikin kaburburansu. Zan kuma komar da su gida zuwa ƙasar Isra'ila.
13
Mutanena za su sani ni ne Ubangiji sa'ad da na buɗe kaburburansu na tashe su daga cikinsu.
14
Zan sa Ruhuna a cikinsu za su kuwa rayu. Zan sa su a ƙasarsu sa'an nan za su sani ni Ubangiji na faɗa, na kuwa aikata.”
15
Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce,
16
“Ɗan mutum, ka ɗauki sanda, ka rubuta a kansa, ‘Domin Yahuza da magoyan bayansa.’ Ka kuma ɗauki wani sanda, ka rubuta a kansa, ‘Domin Yusufu, sandan Ifraimu, da dukan mutanen Isra'ila, magoyan bayansa.’
17
Ka haɗa su su zama sanda guda a hannunka.
18
Sa'ad da kuma jama'arka suka ce maka ka nuna musu abin da kake nufi da waɗannan,
19
sai ka faɗa musu, cewa ni Ubangiji Allah na ce zan karɓe sandan Yusufu, wanda yake a hannun Ifraimu da mutanen Isra'ila magoyan bayansa, in haɗa shi da sandan Yahuza in maishe su sanda guda a hannuna.
20
“Sa'ad da sandunan da ka yi rubutu a kansu suna hannunka a gabansu,
21
sai ka faɗa musu, cewa ni Ubangiji Allah na ce, zan komo da jama'ar Isra'ila daga wurin al'ummai inda suka warwatsu, zan tattaro su daga ko'ina, in maido su ƙasarsu.
22
Zan maishe su al'umma guda a ƙasar Isra'ila. Sarki ɗaya zai sarauce su duka, ba za su ƙara zama al'umma biyu ba, ba kuwa za su ƙara zama masarauta biyu ba.
23
Ba za su ƙara ƙazantar da kansu da gumaka da abubuwan banƙyama da kowane irin laifi ba. Zan komo da su daga riddar da suka yi, in tsarkake su. Za su zama jama'ata, ni kuma zan zama Allahnsu.
24
Bawana Dawuda zai sarauce su. Dukansu za su sami shugaba guda. Za su bi ka'idodina su kiyaye dokokina.
25
Za su zauna a ƙasar da kakanninsu suka zauna, wadda na ba bawana Yakubu. Su da 'ya'yansu da jikokin 'ya'yansu za su zauna a can har abada. Bawana Dawuda kuwa zai sarauce su har abada.
26
Zan ƙulla dawwamammen alkawarin salama da su. Zan sa musu albarka, in yawaita su. Zan kafa Haikalina a tsakiyarsu har abada.
27
Wurin Zamana zai kasance a tsakiyarsu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena.
28
Sa'an nan al'ummai za su sani, ni ne na tsarkake Isra'ila sa'ad da na kafa Haikalina a tsakiyarsu har abada.”
← Chapter 36
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 38 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48