bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Ezekiel 28
Ezekiel 28
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 27
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 29 →
1
Ubangiji ya yi magana da ni ya ce,
2
“Dan mutum, ka faɗa wa Sarkin Taya, cewa Ubangiji Allah ya ce, ‘Da yake zuciyarka ta cika da alfarma, Har ka ce kai allah ne, Kana zaune a mazaunin allah, kana zaune a tsakiyar tekuna, To, kai mutum ne kawai, ba allah ba, Ko da yake ka aza kanka mai hikima ne kamar Allah.
3
Lalle ka fi Daniyel hikima, Ba asirin da yake ɓoye a gare ka.
4
Ta wurin hikimarka da ganewarka ka samo wa kanka dukiya, Ka tattara zinariya da azurfa a baitulmalinka.
5
Saboda yawan hikimarka na yin kasuwanci, ka ƙara dukiyarka, Sai dukiyarka ta sa zuciyarka ta cika da alfarma.’
6
“Saboda haka Ubangiji Allah ya ce, ‘Da yake ka aza kanka mai hikima ne kamar Allah,
7
Don haka zan tura baƙi a kanka, Waɗanda suka fi mugunta cikin sauran al'umma. Za su zare takubansu a kan kyakkyawar hikimarka, Za su ɓara darajarka.
8
Za su jefar da kai cikin rami, Za ka mutu kamar waɗanda suka mutu a tsakiyar teku.
9
Har yanzu za ka ce kai allah ne a gaban waɗanda suke ji maka rauni, Ko da yake kai mutum ne kawai, ba Allah ba?
10
Za ka yi mutuwa irin ta kare ta hannun baƙi, Gama ni Ubangiji Allah na faɗa.’ ”
11
Ubangiji kuma ya yi magana da ni ya ce,
12
“Ɗan mutum, ka yi makoki a kan Sarkin Taya, ka ce Ubangiji Allah ya ce, ‘Kai cikakke ne, cike da hikima da jamali!
13
Kana cikin Aidan, gonar Allah. An yi maka sutura da kowane irin dutse mai daraja, Tare da zinariya. Kana da molo da abin busa. A ranar da aka halicce ka Suna nan cikakku.
14
Na keɓe ka ka zama mala'ika mai tsaro, Kana bisa tsattsarkan dutsen Allah, Ka yi tafiya a tsakiyar duwatsu na wuta.
15
Daga ranar da aka halicce ka ba ka da laifi cikin al'amuranka, Sai ran da aka iske mugunta a cikinka.
16
A wurin yawan kasuwancinka, Ka yi rikici da yawa har ka yi zunubi. Don haka na jefar da kai daga dutsen Allah Kamar ƙazantaccen abu. Na hallaka ka daga tsakiyar duwatsu na wuta, Kai mala'ikan tsaro.
17
Zuciyarka ta yi alfarma saboda kyanka, Ka lalatar da hikimarka ta wurin nuna darajar kanka. Na jefar da kai zuwa ƙasa, Na tone asirinka a gaban sarakuna don su kallace ka.
18
Saboda yawan muguntarka da rashin gaskiyarka cikin kasuwanci, Ka ƙazantar da tsarkakakkun wurarenka. Don haka na sa wuta ta fito daga cikinka, ta cinye ka, Na maishe ka toka a bisa ƙasa a kan idon dukan waɗanda suka kallace ka.
19
Dukan waɗanda suka san ka a cikin al'ummai Za su gigice saboda masifar da ta auko maka, Za ka zama barazana ga al'ummai, Ba za ka ƙara kasancewa ba har abada.”’
20
Ubangiji ya yi magana da ni kuma, ya ce,
21
“Ɗan mutum, ka fuskanci Sidon, ka yi annabci a kanta.
22
Ka ce, Ubangiji Allah ya ce, ‘Duba, ina gāba da ke, ya Sidon, Zan bayyana ikona a cikinki, Za su sani ni ne Ubangiji sa'ad da na hukunta ta, Na bayyana tsarkina a cikinta.
23
Zan aukar mata da annoba da jini a titunanta. Waɗanda za a ji musu rauni da takobi Za su fāɗi matattu a tsakiyarta. Za a tasar mata a kowane waje. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.’ ”
24
“ ‘A kan mutanen Isra'ila kuwa, al'ummai da suke kewaye da su, waɗanda suka raina su, ba za su ƙara zamar musu kamar sarƙaƙƙiya da ƙaya ba. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji Allah.’
25
“Ubangiji Allah ya ce, ‘Sa'ad da na tattara mutanen Isra'ila daga cikin sauran al'umma, inda na watsar da su, na kuma bayyana tsarkina a cikinsu a kan idon al'ummai, sa'an nan za su zauna a ƙarsarsu wadda na ba bawana Yakubu.
26
Za su zauna lafiya a cikinta, za su gina gidaje, su yi gonakin inabi. Za su zauna gonakin inabi. Za su zauna lafiya sa'ad da na hukunta maƙwabtansu waɗanda suka wulakanta su. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji Allahnsu.’ ”
← Chapter 27
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 29 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48