bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Ezekiel 8
Ezekiel 8
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 7
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 9 →
1
A kan rana ta biyar ga wata na shida a shekara ta shida ta zaman talala, sa'ad da nake zaune a gidana, dattawan Yahuza kuma suna zaune a gabana, sai ikon Ubangiji Allah ya sauka a kaina.
2
Da na duba, sai ga siffa wadda dake da kamannin mutum. Daga kwankwason siffar zuwa ƙasa yana da kamannin wuta, daga kwankwason kuma zuwa sama yana da haske kamar na tagulla.
3
Sai ya miƙa hannu, ya kama zankon kaina. Ruhu kuma ya ɗaga ni bisa tsakanin sama da ƙasa, ya kai ni Urushalima cikin wahayi zuwa ƙofar farfajiya ta ciki, wadda take fuskantar arewa, inda mazaunin siffa ta tsokano kishi yake.
4
Sai ga ɗaukakar Allah na Isra'ila a wurin, kamar wahayin da na gani a fili.
5
Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ɗaga idanunka, ka duba wajen arewa.” Na kuwa ɗaga idanuna wajen arewa, na kuma ga siffa ta tsokano kishi a mashigin ƙofar bagade na wajen arewa.
6
Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ga abin da suke yi, abubuwa masu banƙyama da mutanen Isra'ila suke yi a nan don su kore ni nesa da Haikalina? Ai, za ka ga abubuwa masu banƙyama da suka fi haka.”
7
Ya kuma kai ni ƙofar shirayi. Sa'ad da na duba, sai ga wani rami a bangon.
8
Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka haƙa bangon.” Da na haƙa bangon, sai ga ƙofa.
9
Ya ce, mini, “Ka shiga ka ga abubuwan banƙyama da suke aikatawa a nan.”
10
Da na shiga, sai na ga zānen siffofin kowane irin abu mai rarrafe, da haramtattun dabbobi, da dukan gumakan mutanen Isra'ila kewaye da bangon.
11
Dattawan Isra'ila saba'in suna tsaye a gabansu. Yazaniya ɗan Shafan yana tsaye tare da su. Kowa yana riƙe da farantin ƙona turare. Hayaƙin turaren ya tunnuƙe zuwa sama.
12
Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum ko ka ga abin da dattawan Isra'ilawa suke yi a cikin duhu? Kowa yana cikin ɗakin zānannun siffofin gumaka, sukan ce, ‘Allah ba ya ganinmu. Ubangiji ya rabu da ƙasan nan.”’
13
Ya kuma ce mini, “Har yanzu dai za ka ga abubuwa masu banƙyama da suka fi haka waɗanda suke aikatawa.”
14
Sai ya kai ni a bakin ƙofar arewa ta Haikalin Ubangiji, ga kuwa mata a zaune suna kuka domin gunkin nan, Tammuz.
15
Sa'an nan ya ce mini, “Ya ɗan mutum, ka ga wannan? Har yanzu ma za ka ga abubuwan da suka fi waɗannan banƙyama.”
16
Ya kuma kai ni farfajiya ta can cikin Haikalin Ubangiji. Na ga mutum wajen ashirin da biyar a ƙofar Haikalin Ubangiji a tsakanin shirayi da bagade, suka juya wa Haikalin Ubangiji baya, suka fuskanci wajen gabas, suna yi wa rana sujada.
17
Ya kuma ce mini, “Ya ɗan mutum, ka ga wannan? Wato mutanen Yahuza ba su mai da aikata abubuwa masu banƙyama nan wani abu ba. Sun cika ƙasar da hargitsi, suna ta tsokanar fushina. Ga shi, suna hura hanci a gabana.(Eze 9.9; Eze 16.26
18
Zan yi hukunci mai zafi, ba zan yafe ba, ba kuma zan ji tausayi ba, ko da yake suna kuka da babbar murya a kunnuwana ba zan ji su ba.”
← Chapter 7
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 9 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48