bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Ezekiel 6
Ezekiel 6
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 5
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 7 →
1
Ubangiji ya yi magana da ni ya ce,
2
“Ya ɗan mutum, ka zuba ido wajen duwatsun Isra'ila, sa'an nan ka yi annabci a kansu.
3
Ka ce musu, ‘Ya ku duwatsun Isra'ila, ku ji maganar Ubangiji Allah! Haka Ubangiji Allah ya ce a kan duwatsu, da tuddai, da kwazazzabai, da kwaruruka. Ga shi, ni kaina, zan kawo takobi a kanku, zan hallaka wuraren tsafinku.
4
Bagadanku za su zama kango, za a farfasa bagadanku na ƙona turare, zan sa kisassunku su faɗi a gaban gumakansu,
5
zan sa gawawwakin Isra'ilawa a gaban gumakansu, zan warwatsa ƙasusuwanku kewaye da bagadanku.
6
A duk inda kuke zaune, biranenku za su zama kango, wuraren tsafinku da bagadanku za su lalace, gumakanku da bagadanku na ƙona turare za a farfashe su. Za a shafe dukan abin da kuka yi.
7
Za a kashe waɗansu daga cikinku sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji.
8
“‘Duk da haka zan bar waɗansunku da rai, gama waɗansu daga cikinku za su tsere wa takobi, amma zan watsa su cikin sauran al'umma.
9
Waɗansunku da suka tsere za su tuna da ni cikin al'ummai inda aka kai su bautar talala yadda raina ya ɓaci saboda zuciyarsu ta rashin imani wadda ta rabu da ni, da idanunsu masu zina da suke bin gumaka. Za su kuwa ji ƙyamar kansu saboda mugayen abubuwa da suka aikata.
10
Za su kuma sani, ni Ubangiji, ba a banza na ce zan kawo musu wannan masifa ba.”’
11
Ubangiji Allah ya ce, “Ka tafa hannunka, ka ɗage ƙafarka, sa'an nan ka ce, ‘Kaito, kaito, saboda dukan mugayen abubuwan ƙyama da mutanen Isra'ila suka yi, gama takobi, da yunwa, da annoba za su kashe su.
12
Annoba za ta kashe wanda yake nesa, wanda yake kusa kuwa takobi zai kashe shi. Yunwa kuma za ta kashe wanda yaƙi ya kewaye shi. Ta haka zan aukar da fushina a kansu.
13
Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji, sa'ad da gawawwakinsu sun kwanta tare da gumakansu kewaye da bagadansu a kan kowane tudu, da kan tsaunuka, da ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa, da ƙarƙashin itacen oak mai ganye, duk inda suka miƙa turare mai ƙanshi ga dukan gumakansu.
14
Zan nuna ikona a dukan ƙasar, in mai da ita da wuraren zamansu duka hamada. Ƙasarsu za ta zama hamada har zuwa Dibla. Kowa zai sani ni ne Ubangiji.”’
← Chapter 5
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 7 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48