bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Ezekiel 7
Ezekiel 7
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 6
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 8 →
1
Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
2
“Ya kai, ɗan mutum, ni Ubangiji Allah, na ce wa ƙasar Isra'ila, matuƙa ta yi a kan kusurwa huɗu na ƙasar!
3
“Yanzu matuƙarki ta yi. Zan fashe fushina a kanki, zan kuma shara'anta ki bisa ga ayyukanki, in hukunta ki saboda dukan ƙazantarki.
4
Ba zan yafe miki ba, ba kuwa zan ji tausayinki ba, amma zan hukunta ki saboda ayyukanki sa'ad da kike tsakiyar aikata ƙazantarki. Sa'an nan za ki sani ni ne Ubangiji.”
5
Ubangiji Allah ya ce, “Masifa a kan masifa, ga shi, tana zuwa!
6
Matuƙa ta yi, ta farka a kanki, ga shi, ta yi!
7
Ƙaddararku ta auko muku, ya ku mazaunan ƙasar. Lokaci ya yi, rana ta gabato, ranar tunzuri, ba ta murna da ta sowa a kan duwatsu ba.
8
“Yanzu, ba da jimawa ba, zan fashe hasalata a kanku, in aukar da fushina a kanku, in hukunta ku bisa ga ayyukanku. Zan hukunta ku saboda dukan ƙazantarku.
9
Ba zan yafe ba, ba kuwa zan ji tausayi ba, amma zan hukunta ku bisa ga ayyukanku sa'ad da kuke tsakiyar aikata ƙazantarku, sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji wanda yake hukunta ku.
10
“Ga rana ta zo. Ƙaddararku ta zo, rashin gaskiya ta yi fure, girmankai kuma ya yi toho.
11
Hargitsi ya habaka, ya zama sandan mugunta. Ba wanda zai ragu cikinsu, ko yawaitarsu, ko dukiyarsu, ko wani muhimmi a cikinsu.
12
“Lokaci ya yi, ranar ta gabato, kada mai saye ya yi farin ciki, kada kuma mai sayarwa ya yi baƙin ciki, gama fushina yana kan taron jama'a duka.
13
Mai sayarwa ba zai ta da ciniki ba sa'ad da suke da rai, gama fushina yana bisa kan dukan taron jama'arsu, ba zai fasa ba. Ba wanda yake zamansa cikin zunubi da zai iya shiryar da kansa.”
14
“Sun busa ƙaho, sun gama shiri duka, amma ba wanda ya tafi yaƙi, gama fushina yana kan dukan taron jama'a.
15
Takobi yana zare a waje, annoba da yunwa suna ciki. Wanda yake waje takobi zai kashe shi, wanda kuma yake ciki annoba da yunwa za su kashe shi.
16
Idan akwai waɗanda suka tsere, za a same su a kan duwatsu kamar kurciyoyin kwaruruka, suna baƙin ciki dukansu, kowa yana baƙin ciki saboda laifinsa.
17
Dukan hannuwa sun raunana, dukan gwiyoyi kuma sun zama marasa ƙarfi kamar ruwa.
18
Sun sa tufafin makoki, razana ta kama su, fuskokinsu kuma suna cike da kunya, akwai sanƙo a kawunansu.
19
Sun watsar da azurfarsu a titi, zinariyarsu kuma ta zama kamar ƙazantacciyar aba. Azurfarsu da zinariyarsu ba za su iya cetonsu ba, a ranar fushin Ubangiji. Ba za su iya ƙosar da su ba, gama su ne sanadin tuntuɓensu.
20
Suna fariyar banza da kyawawan kayan adonsu, na zinariya da azurfa. Da su suka yi siffofi masu banƙyama, da ƙazantattun abubuwa. Domin haka zan maishe su ƙazantattun abubuwa a gare su.
21
“Zan ba da su ganima ga baƙi, da kwaso ga mugayen mutanen ƙasar. Za su lalatar da su.
22
Zan kuwa juya daga gare su. Zan bar su su ƙazantar da Haikalina. Mafasa za su shiga su ƙazantar da shi.
23
“Sai ka ƙera surƙa, gama ƙasar tana cike da alhakin jini, birnin kuma yana cike da hargitsi.
24
Zan kawo al'ummai masu muguntar gaske su mallaki gidajensu. Zan sa fariyar masu ƙarfi ta ƙare. Za a ƙazantar da masujadansu.
25
Sa'ad da wahala ta zo, za su nemi salama, amma ba za su same ta ba.
26
Masifa a kan masifa, jita-jita a kan jita-jita. Suna neman wahayi daga wurin annabi, amma doka ta lalace a wurin firist, shawara kuma ta lalace a wurin dattawa.
27
Sarki yana makoki, yarima kuma zai fid da zuciya. Hannuwan mutanen ƙasar sun shanye saboda razana. Zan sāka musu bisa ga ayyukansu, zan kuma hukunta su kamar yadda suka hukunta waɗansu. Za su kuwa sani ni ne Ubangiji.”
← Chapter 6
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 8 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48