bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Ezekiel 30
Ezekiel 30
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 29
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 31 →
1
Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce,
2
“Ɗan mutum, ka yi annabci, ka ce Ubangiji Allah ya ce maka ka yi kuka, kana cewa, ‘Kaito, kaito saboda wannan rana!’
3
Gama ranar ta gabato, Ranar Ubangiji ta yi kusa, Rana ce ta gizagizai, Ranar halakar al'ummai.
4
Takobi zai fāɗa a kan Masar, Azaba kuma za ta sami Habasha. Za a kashe mutane a Masar, Za a kwashe dukiyarta, A rushe harsashin gininta.
5
“Yaƙi zai ci Habasha, da Fut, da Lud, da dukan Arabiya, da Libya, da mutanen ƙasar da suka haɗa kai da su.”
6
Ubangiji ya ce, “Waɗanda suke goyon bayan Masar za su fāɗi. Ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare. Za a kashe su da takobi tun daga Migdol zuwa Sewene.
7
Za ta zama kufai fiye da sauran ƙasashe, Biranenta kuma za su zama kufai, marar amfani, fiye da sauran birane.
8
Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, Sa'ad da na kunna wuta cikin Masar, Na kuma kakkarya dukan masu taimakonta.
9
“A ranan nan manzanni masu sauri za su fito daga wurina a jiragen ruwa, su tsoratar da Habashawa, ba zato. Azaba za ta auko a kansu a ranar hallakar Masar. Ga ta nan, ta zo.”
10
Ubangiji Allah ya ce, “Zan sa dukiyar Masar ta ƙare Ta hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila,
11
Shi da mutanensa, Mutane mafi bantsoro a cikin sauran al'umma, Za a kawo su don su hallakar da ƙasar. Za su zare takubansu a kan Masar, Su cika ƙasar da gawawwaki.
12
Zan busar da Kogin Nilu, Zan kuma sayar da ƙasar ga mugaye. Zan sa ƙasar ta lalace Da dukan abin da yake cikinta, Ta hannun baƙi, Ni Ubangiji, na faɗa.”
13
Ubangiji Allah ya ce, “Zan hallakar da gumaka Da siffofi a Memfis. Ba za a ƙara samun hakimi a ƙasar Masar ba, Saboda haka zan aukar da tsoro a ƙasar Masar.
14
Zan sa Fatros ta zama kufai, Zan kunna wa Zowan wuta, Zan kuma shara'anta No.
15
Zan kwarara hasalata a kan Felusiyum, Wato kagarar Masar, Zan datse jama'ar No.
16
Zan kunna wa Masar wuta. Felusiyum za ta sha azaba mai tsanani, No kuwa za a tayar mata da hankali, Za a rurrushe garukanta. Za a tasar wa Memfis dukan yini.
17
Samarin Awen da na Fi-beset Za a kashe su da takobi, Matan kuma za su tafi bauta.
18
A Tafanes rana za ta yi duhu, Sa'ad da na karya mulkin ƙasar Masar, Ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare, Za a rufe ta da gizagizai. 'Ya'yanta mata kuwa za a kai su bauta.
19
Ta haka zan hukunta Masar, Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.”
20
A kan rana ta bakwai ga watan fari, a shekara ta goma sha ɗaya, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
21
“Ɗan mutum, na karya hannun Fir'auna, Sarkin Masar, ga shi, ba za a ɗora hannun ba, don kada ya warke ya zama da ƙarfi yadda zai iya riƙon takobi.”
22
Ubangiji Allah kuma ya ce, “Ina gāba da Fir'auna, Sarkin Masar, zan karya hannuwansa duka biyu, da lafiyayyen da kuma wanda na riga na karya. Zan sa takobinsa ya faɗi daga hannunsa.
23
Zan watsar da Masarawa a cikin sauran al'umma, in kuma warwatsa su a ƙasashen duniya.
24
Zan ƙarfafa hannun Sarkin Babila, in sa takobina a hannunsa, amma zan karya hannuwan Fir'auna, zai yi nishi a gaban Sarkin Babila, kamar mutumin da aka yi wa raunin ajali.
25
Zan ƙarfafa hannuwan Sarkin Babila, amma hannuwan Fir'auna za su shanye. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na sa takobina a hannun Sarkin Babila, shi kuwa zai miƙe shi a kan ƙasar Masar.
26
Zan watsar da Masarawa a cikin sauran al'umma, in warwatsa su a ƙasashen duniya. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.”
← Chapter 29
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 31 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48