bible
ra
🌐 Language
English
Español
Français
Deutsch
Português
Italiano
Nederlands
Русский
中文
日本語
한국어
العربية
Türkçe
Tiếng Việt
ไทย
Indonesia
All Languages
Home
/
Hausa
/
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
/
Ezekiel 24
Ezekiel 24
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
← Chapter 23
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 25 →
1
A kan rana ta goma ga watan goma, a shekara ta tara, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
2
“Ɗan mutum, ka rubuta sunan wannan rana. Ranar ke nan da Sarkin Babila ya kewaye Urushalima da yaƙi.
3
Ka yi wa 'yan tawayen nan magana da misali, ka faɗa musu cewa, ni Ubangiji na ce, ‘Ka ɗora tukunya, ka ɗora ta a wuta, Ka cika ta da ruwa.
4
Ka zuba gunduwoyin nama a ciki, Dukan gunduwoyi masu kyau, wato cinya da kafaɗa, Ka cika ta da tantakwashi.
5
Ka kama mafi kyau daga cikin garken, Ka sa sauran ƙasusuwa a ƙarƙashinsa, Ka tafasa gunduwoyin, Ka kuma tafasa tantakwashin.’
6
“Ni Ubangiji Allah na ce, ‘Domin haka kaiton birnin nan mai zubar da jini, Da tukunya wadda take da tsatsa, Wadda tsatsarta ba ta fita cikinta ba! Ka sa sauran ƙasusuwa a ƙarƙashinsa, Kada ka yi zaɓe.
7
Gama jinin da ta zubar yana tsakiyarta, Ta zubar da shi a kan dutse, Ba ta zubar da shi a ƙasa inda za ta rufe shi da ƙura ba.
8
Don a tsokani fushina har in yi sakayya, Na zuba jinin da ta zubar a kan dutse, Don kada a rufe shi.’
9
“Saboda haka, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Kaitonka, ya birni, mai zubar da jini! Ni kuma zan tsiba itace da yawa.
10
Ka tula gumagumai, ka kunna wuta, Ka tafasa naman sosai, Ka zuba kayan yaji a ciki, Ka bar ƙasusuwan su ƙone.
11
Ka ɗora tukunyar da ba kome cikinta a bisa garwashi Domin ta yi zafi, tagullarta ta yi ja wur, Domin dauɗarta ta narke a ciki, Tsatsarta kuma ta ƙone.
12
Ta gajiyar da ni a banza, Wutar ba ta fitar da yawan tsatsarta ba.
13
Ya Urushalima, tsatsarki ita ce ƙazantar lalatarki. Da yake na tsabtace ki, ba ki tsabtatu ba, To, ba za ki ƙara yin tsabta ba, Har lokacin da na fashe fushina a kanki.’
14
Ni, Ubangiji na faɗa, zai tabbata gama zan aikata, ba zan fasa ba, ba kuwa zan ƙyale ba, ba kuma zan bari ba. Zan hukunta ki saboda hanyoyinki da ayyukanki, ni Ubangiji Allah na faɗa ”
15
Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,
16
“Ya ɗan mutum, ga shi, ina gab da ɗauke maka ƙaunatacciyarka farat ɗaya, amma fa, kada ka yi makoki, ko kuka, ko ka zubar da hawaye.
17
Ka yi ajiyar zuciya a hankali, kada ka yi makoki saboda matacciyar. Ka naɗa rawaninka, ka sa takalmanka, kada ka ja amawali, kada kuma ka ci abincin masu makoki.”
18
Sai na yi magana da mutane da safe, da maraice kuwa matata ta rasu. Kashegari da safe, sai na yi kamar yadda aka umarce ni.
19
Mutane kuwa suka tambaye ni dalilin da ya sa nake yin haka.
20
Sai na ce musu, “Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
21
in faɗa wa mutanen Isra'ila, cewa Ubangiji Allah ya ce, ‘Zan ƙazantar da Haikalina, abin fariyarku, da abin da idanunku suke jin daɗin ganinsa, da abin faranta zuciyarku. 'Ya'yanku maza waɗanda kuka bari a baya, za a kashe su da takobi.
22
Za ku kuwa yi kamar yadda na yi, wato ba za ku ja amawali ba, ba kuwa za ku ci abincin masu makoki ba.
23
Za ku naɗa rawunanku, ku sa takalmanku, ba za ku kuma yi makoki ko kuka ba, amma za ku lalace cikin zunubanku. Za ku yi ta nishi.
24
Da haka Ezekiyel zai zama muku alama. Za ku yi kamar yadda ya yi duka. Sa'ad da wannan ya faru, za ku sani nine Ubangiji Allah.’
25
“Kai ɗan mutum, a ranar da zan ɗauke musu madogararsu, da murnarsu, da darajarsu, da abin da idanunsu suka ji daɗin gani, da abin da yake faranta zuciyarsu, da 'ya'yansu mata da maza,
26
a wannan rana wanda ya tsere zai kawo maka labarin.
27
A ranar bakinka zai buɗe, za ka yi magana da wanda ya tsere, ba kuma za ka zama bebe ba. Da haka za ka zama alama gare su, za su kuwa sani ni ne Ubangiji.”
← Chapter 23
Jump to:
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 25 →
All chapters:
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48